Da gangar Westerhof ya ki tafiya dani gasar cin kofin duniya a 1994 – Tijjani Babangida

0

Fitaccen ɗan wasan Super Eagles na Najeriya, Tijjani Babangida ya bayyana cewa da kociyan kungiyar ƙwallon ƙafa na Najeriya a wancan lokaci Clement Westerhof ya tafi da shi gasar wasan cin kofin kwallain kafa ta duniya da aka buga a 1994, da Najeriya ta wuce matakin zango na biyu.

Babangida ya ce, dalilin da yasa ba a tafi da sh ba kuwa shine don ya ki yarda ya zama manajar sa shi ne yasa ya ki saka shi cikin wannan tim din.

” A wannan lokaci ina buga kwallon kafa a Roda JC, dake kasar Netherland, nine wanda ya fi kowa cin kwallo ta gefe a duniya saboda ina da gudun gaske. Amma da gangar ya ki saka ni ciki tim din.

Babangida ya ce a wancan lokacin da an tafi da shi da a lokacin da Amokachi da Amunike suka ji ciwo shi ne za musanya daya daga cikin su da shi.

Sai dai kuma abokanan hirar sa a lokacin da Jaridar Punch ke hira da shi, Amunike da Okocha, cikin raha, sun ce koda an tafi dashi World Cup din babu inda za a saka shi, domin tim din garau take.

” Ba karya bane ka iya taka leda a lokacin amma kuma baka da wuri ne a tim din. Kusan duka ƴan wasan kokarin su ne ya basu wuri ba sanin wani ko gata ba.

Share.

game da Author