Cutar mu aka yi, amma mun fi karfin Chelsea – In ji magoya bayan Madrid

0

Mabiya bayan Kungiyar kwallon kafan Real Madrid musamman Najeriya sun yi korafin wai alkalin wasa ne ya murde musu wasa ya ri rika baiwa Chelsea dama har ta yi nasara a kan su.

Chelsea ta yi ragaraga da Madrid a wasan kusa da na karshe na gasar Champions League da aka buga a filin Chelsea dake Ingila.

Dama kuma a wasan farko da aka buga a Madrid, kasar Spain, Chelsea ta buga Kunnen doki da Madrid.

A haduwa ta biyu, Chelsea ta nuna wa Madrid ba sani ba sabo, domin tun a tashin farko ta rika kai wa Madrid Luguden hare-haren da kwallo a ragar ta kafin a karshe bayan duk ta gama birkita mata kwakwalwa sai kwallo daya ya shiga ragar Madrid.

Gab da za a tashi wasa kuma kwallo ta biyu ta shiga.

Kurunkus, kungiyar Chelsea da Manchester City za su buga wasan karshe a karshen wannan wata.

Share.

game da Author