Sakamakon jarabawar tantance ‘yan takara da jam’iyyar APC ta yi wa duka wadanda suka sayi fom din tsayawa takarar shugabannin Kananan hukumomin jihar da Kansiloli ya fito, sai dai bai yi wa wasu dadi ba.
A bisa jadawalin sakamakon jarabawar, Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa Saleh Shuaibu, ya sha kasa a wannan jarabawa.
Sakamakon jarabawar ya nuna wai an taba samun sa dymu-dumu cikin harkallar wasu kudaden karamar hukumar.
Shi ko Abubakar Buba na karamar hukumar Lere da Mahmood Mohammed na Soba wanda shine shugaban kungiyar shugabannin Kananan hukumomin jihar, duk sun fadi jarabawar ne saboda samun su da aka yi da yi wa jam’iyya zagon kasa da yi wa wata jam’iyyar aiki a boye.
Sakamakon jarabawar ya nuna an wancakalar da masu neman tsayawa takarar kujerar shugabannin kananan hukumomi da suka sayi fom, naira miliyan 1.1 38.
Cikin ‘yan takara 115, mutum 75 ne suka ci jarabawa, 38 sun fadi, wasu biyu da suka ji wannan karon sai an yi jarabawa karkashin farfesoshi har hudu, suka shafa wa kansu ruwa, ko fom din ma ba su mayar ba.
Wasu da zuka zanta da wakiln PREMIUM TIMES HAUSA a Kaduna sun bayyana jin dadin su game da wannan tsari da jam’iyyar APC ta fito da shi.
” Ni dai a nawa ganin wannan tsari yayi kyau matuka domin zai baiwa wadanda suka dace damar tsaya wa takara a jihar.” In ji Umar Muhammed.
Za ayi zaben kananan hukumomin jihar Kaduna a farkon watan gobe.
Discussion about this post