CHAMPIONS LEAGUE: Chelsea ta kafa tarihi, ta jefa Manchester City cikin wani kwandon tarihi

0

Lashe Kofin Champions League da Chelsea ta ya, inda ta yi nasara da ci 1:0 kan Manchester City, ta ƙara cefa ƙungiyar City cikin kwandon sharar tarihi.

Rashin nasarar da Man City ta yi, ya nuna cewa wasannin ƙarshe bakwai kenan a jere, ana doke ƙungiyar da ta kai ga buga wasan ƙarshe a tarihin shiga gasar ƙungiyar.

Cikin shekarar 2000, Valencia ta kai wasan ƙarshe a karon farko, amma ta sha kashi.

Cikin shekarar 2002, Bayern Leverkusen ta kai ga wasan ƙarshe, amma ta sha duka a hannun Real Madrid da ci 2:1.

Sai kuma ƙungiyar FC Monaco da kai ƙarshe a gasar 2004. Ita ma ba ta samu nasara ba, shan kashi ta yi.

A shekarar 2006, a karon farko Arsenal ta kai wasan ƙarshe. Sai dai kuma ta kasa lashe kofin, a yayin karawar ta da FC Barcelona.

Cikin 2008 Chelsea ta kai wasan ƙarshe, amma ba ta yi nasara ba. Sai a karo na biyu da ta kai wasan ƙarshe ne ta yi nasara.

Ƙungiyar Tottenham ta kai wasan ƙarshe cikin 2019 a karon farko, amma ta yi rashin nasara a hannun Liverpool FC.

Ƙungiyar PSG ta samu nasarar kaiwa ga wasan ƙarshe a shekarar 2020 a karon farko. Amma Bayern Munich ta jefa mata ƙwallo ɗaya da ya maƙale, ya hana ta cin kofi.

2021 kuma a karon farko Manchester City ta kai wasa na ƙarshe, amma Chelsea ta jefa mata ƙwallo ɗaya da ya maƙale mata a maƙoshi, ya hana ƙungiyar ɗaukar kofi.

Share.

game da Author