Buhari zai sake kinkimo bashin naira tiriliyan 2.343

0

Shugaba Muhammadu Buhari na neman amincewar sake narko bashin dala biliyan 6.1 daga kasashe da manyan cibiyoyin hada-hadar kudade na duniya, domin a samu kudaden da za a yi ayyukan kasafin 2021 da su.

Cikin wata wasika da Bhhari ya aika wa Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya a ranar Talata, shugaban wanda ya yi kaurin suna wajen ciwo bashi ya roki majalisun biyu su amince masa ya ciwo bashin.

Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya Idris Wase ne ya kadanta takardar a ranar Talata din nan a zauren Majalisar Tarayya.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya karanta wasikar a Majalisar Dattawa a ranar Talata din.

Idan aka canja dala da naira, adadin kudaden da Buhari ke neman kara ciwowa bashi zun kai naira tiriliyan 2 da biliyan 343.

Domin naira daya na daidai da naira 379, farashin gwamnati.

Kasafin 2021 dai ya samu gibin naira tiriliyan 5 da biliyan 600.

Share.

game da Author