Akalla fasinjoji 28 aka tabbatar da sun halaka, a lokacin da wani jirgin ruwa mai dauke da mutum 100 ya tintsire a cikin ruwa, a cikin Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Babban Daraktan Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Ahmed Inga ya bayyana cewa lamarin ya faru a ranar Asabar a lokacin da jirgin ya kusa yada zango inda zai sauke fasinjojin, wadanda ya dauko daga kauyen Zumba da Tija na cikin Karamar Hukumar Munya.
Hatsarin inji Inga ya faru ne lokacin da jirgin ya kusa kai bakin ganga, amma sai ya tunkuyi wani kwauren itace da ke a cikin ruwan, ya tirtsire.
“Mutum 65 sun tsira, wasu 28 sun mutu amma masu nutson ceto cikin ruwa daga kauyen da abin ya faru, sun yi nutso sun tsamo gawarwakin 28.
“Sai dai har yanzu ba a ga wasu mutum bakwai ba. Duk da dai masu ceto ba su hakura ba, su na ci gaba da laluben su a cikin ruwa.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iayalai da ‘yan uwan wadanda jirgin ruwa ya kife da su a Shiroro jihar Neja.
Shugaba Buhari yayi addua’ar Allah ya ji kan su.
Discussion about this post