Buhari na nuna wa ‘Yan kudu bambamci a wajen nada manyan mukaman gwamnati – Gwamna Bala

0

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana cewa yana tare da gwamnonin yankin kudancin Najeriya 100 bisa kan yadda Buhari ke nuna fifiko ga ‘yan Arewa fiye da’ yan Kudu wajen raba mukamai.

Shafin Rueben Abati, dake yanar ta wallafa wadanan kalamai na gwamna Bala, inda jaridar ta kara da cewa gwamnan ya jaddada korafin da ake yi wai gwamnati ta na nuna fifiko da son kai ga ‘yan Arewa, yan kudu kuma ko oho.

Idan ba’ a manta ba, gwamnonin Kudu sun zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da nuna fifiko a wajen nade-naden mukaman gwamnati ga ‘Yan Arewa nada ‘yan Arewa bai damu da ya nada ‘ yan kudu manyan mukamai ba.

Sannan sun zayyana wasu bukatu 12 da suke neman gwambati Buhari ta gaggauta biya musu ko ta halin kaka.

” Akwai kanshin gaskiya a abubuwan da gwamnonin kudu ke zargin gwamnatin Buhari da yi na nuna fifiko ga yankin Arewa fiye da kudancin kasar nan.

” Abinda muka sani shine irin mulkin da muke yi a kasar nan shine na raba daidai, amma ba haka Buhari ke yi ba. Dole sai an saita komai daidai daga can sama tukunna, idan ba haka ba kuwa, ba za a taba samun cigaba mai ma’ana ba a kasar.

Yaki da cin Hanci da Rashawa

Gwamna Bala ya yi tir da salon yaki da cin hanci da rashawa ta wannan gwamnati, yana mai cewa, akwai wasu shafaffu da mai da ba a taba sannan, dauki daidai ake yi, an bar wasu yan gaban goshin gwamnati na sheke ayarsu.

” Ni fa a ganina wannan gwamnati, gwamnatin Buhari tuni ta saki layi, kwakwalwar ta dode, bata san yadda za ta yi ta farfado da tattalin arzikin kasar nan ba. Babu abin da suka iya yi yanzu sai su ce wancan yayi kaza, wancan ne ke yi wa gwamnatin zagon kasa, wancan ke bada mana kasa a ido, gashinan dai gaba daya basira ta kare musu.

Share.

game da Author