Buba Galadima ya karyata zargin ya na zawarcin PDP, ya ce rAPC za ta dawo ta girgiza siyasar Najeriya

0

Tsohon babban makusancin Shugaba Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ya karyata ji-ta-ji-tar ya na, zawarcin APC ko PDP.

Galadima ya yi wannan jawabi a wurin taron “Makoma da Kalubalen Jam’iyyun Siyasa”, inda ya ce shi tuni ya fice daga APC, kuma ba ɗan PDP ba ne shi.

Taron wanda Cibiyar Binciken Ƙwaƙwaf ta PREMIUM TIMES ce ta shirya shi, Buba Galadima ya bayyana kan sa a matsayin Shugaban ballallun jam’iyyar APC, wato rAPC.

Kuma ya ƙara da cewa “rAPC na kan hanyar dawowa fagen siyasa kuma za ta girgiza manyan jam’iyyun ƙasar nan, manya da ƙanana.”

“Ina so na yi babban gyara a nan. Ni ba ɗan jam’iyyar PDP ba ne. Kuma ni ba ɗan jam’iyyar APC ba ne. Ni ne Shugaban rAPC na ƙasa baki ɗaya.” Inji Buba Galadima.

“Kuma ina sanar da cewa kwanan nan za su sake yunƙurowa mu jinjiga fagen dagar siyasar ƙasar nan.”

A wurin taron, Buba Galadima ya ce daga 1999 zuwa yau, ‘yan siyasar Najeriya ciki har da shi, sun kasa ɗaukar darasin da ya kamata su ɗauka.

Shi da sauran mutum uku da su ka tattauna ƙalubalen da ya addabi siyasar Najeriya, sun amince cewa, “har yanzu siyasa da dimokraɗiyya rarrafe su ke yi a Najeriya, saboda har yau dai kuɗi da kuma tilasta ɗan takara ke tasiri a zabe, ba cancanta da ƙwarewa ba.”

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ce ta shirya taron.

Sauran waɗanda su ka yi jawabi a wurin taron, sun haɗa da Ezenwa Nwagwu, wanda ke Cibiyar PAACA. Ya ce yankewar zumunci da cuɗanya tsakanin jam’iyya mai mulki da sauran manya da ƙananan jam’iyyun adawa ta samo asali ne tun hawan mulkin Olusegun Obasanjo, a 1999.

Ezanwa ya nemi a dawo da wannan tsarin.

Idayat Hassan ta CCD kuwa cewa ta yi jam’iyyun siyasa a Najeriya sun zubar da ƙima da mutuncin su na kasancewar su makarantun koyon darussan dimokraɗiyyar da yanzu ta ce ba su koyar da wani darasin dimokraɗiyya mai muhimmanci.

Share.

game da Author