BOKO HARAM: Za a fara shari’ar ‘yan ta’adda 800 – Gwamnatin Tarayya

0

Akalla mutum 800 ne za a fara shari’ar su bisa tuhumar da za a yi masu kan ayyukan ta’addanci, da zaran an janye yajin aikin da ma’aikatan kotunan kasar nan ke kan yi.

Wani jami’in gwamnati ya ce ‘yan ta’addar su 800 na cikin 1,000 wadanda masu gabatar da kara na Ma’aikatar Shari’a su ka yi nazarin fayil-fayil din su.”

Wadanda za a gurfanar din dai yanzu haka duk su na tsare ne a gadurum din sojoji a sansanoni daban-daban a Maiduguri, Jihar Barno.

Mataimakin Darakta Mai Kula da Shari’u Masu Tsauri a Ma’aikatar Shari’a ta Kasa, Chioma Onuegbu ce ta bayyana haka a Abuja, a wani bada horo da su ka yi wa manema labarai masu dauko rahotannin bangaren, wanda Gidauniyar Wayamo Foundation ta shirya.

“Daga cikin mutane 1000 da bangaren gabatar da kara su ka binciki fayil din su, an gamsu da cewa 800 a cikin su na da laifukan ta’addancin da za a iya gurfanar da su a gaban alkali.

“Amma an bayyana cewa za a saki guda 170 saboda ba a same su da shaidar aikata laifin komai ba.

“Daga cikin 800 din kuma tuni an mika fayil-fayil na shari’ar da za a fara yi wa mutum 280.”

Ta kara da cewa Hukumar Lauyoyi ta ‘Legal Aid Council of Nigeria (LACON), ce za ta kare ‘yan Boko Haram din a kotu.

PREMIUM TIMES ta gano cewa ‘yan Boko Haram din su 800 da za a fara shari’ar su, ‘yan kalilan ne idan aka yi la’akari da dubban wadanda ke tsare a hannun sojoji a Maiduguri da Kainji.

Share.

game da Author