Birtaniya ta maido wa Najeriya fam miliyan 4.2 na kudaden da tsohon gwamnan Jihar Delta, James Ibori da makusantan sa da iyalan sa su ka sace su ka boye a can kasar.
Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana haka ranar Talata a Abuja.
An maido kudaden makonni biyu bayan Malami ya bayyana cewa kudaden su na kan hanya, amma ana samun jinkiri ne a bankunan kasashen waje, inda ake bata lokacin rubuce-rubuce da cike-ciken takardu a bankuna.
Amma a ranar Talata Malami ya fitar da sanarwa ga manema labarai cewa bankunan sun tura wa Najeriya naira wadda sun kai daidai da fam 4,214,017.66, tun a ranar 10 Ga Mayu.
Umar Gwandu, Kakakin Minista Malami ne ya bayyana sanarwar dawo da kudaden cikin asusun gwamnatin tarayya. Sai dai bai ce ga adadin ko nawa ne kudaden ba bayan da aka maida su naira.
Sai dai kuma lissafin da PREMIUM TIMES ta yi, ya nuna kudin za su iya kaiwa naira biliyan 2.4 a farashin fam a CBN, ko kuma naira biliyan 2.9 a farashin kasuwar tsaye ta ‘yan canji.
PREMIUM TIMES ta taba buga labarin cewa Gwamnatin Najeriya da ta Birtaniya sun sa hannun yarjejeniyar dawo da wasu kudade daga kasar, wadanda idan aka canja su zuwa naira, za su iya kai naira biliyan 2.4.
An sa wa yarjejeniyar hannu ce a Ma’aikatar Shari’a ta Najeriya, inda Minista Malami ya sa hannu a madadin gwamnatin Najeriya.
Jakadan Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing ce ta sa hannu a madadin Birtaniya.
Yayin da ya ke sa hannu a kan yarjejeniyar, Minista Malami ya ce za a yi amfani da kudaden wajen aikin titin Lagos zuwa Abuja da kuma titin Abuja zuwa Kano da kuma aikin Gadar Kogin Neja.
Sai dai kuma Gwamnatin Jihar Delta ta ce ita ya kamata a maida wa kudaden, domin hakkin jihar Delta ne kuma ‘yan jihar Delta din ne su ka sace kudaden.
Discussion about this post