BIRI YA KAI GA ASHANA: Sunday Igboho ya yi barazanar hargitsa zaben 2023 a Jihohin Yarabawa

0

Tantirin dan ta-kifen yankin Yarabawa, Sunday Igboho ya yi barazanar hargitsa zaben 2023 a dukkan jihohin Kudu maso Yamma.

Igboho ya yi wannan cika-baki a Osogbo, babban birnin jihar Osun, wurin gangamin rajin ballewa daga Najeriya, a ranar Asabar.

Ya yi ikirarin cewa gwamnonin jihohin Yarabawa da dama na son ballewa daga Najeriya, amma su na tsoron idan su ka fito fili su ka ayyana bukatar su, za a daina turo masu kudade daga gwamnatin tarayya.

Ya ce gwamnonin na goyon bayan kafa Kasar Yarabawa, amma tsoro ya hana su fitowa su furta.

“Ba mai iya rufe min baki ko yi min wata barazanar tsorata ni. Mu yanzu ba a cikin Najeriya mu ke ba. Babu ruwan mu da Najeriya. Kuma ba za mu sake hadewa da su ba.” Inji Sunday Igboho.

“An gama zabe da sunan Najeriya a yankin Yarabawa. Idan ku ka ga an yi zabe a nan, to ku tabbatar zaben Kasar Yarabawa ne aka yi. Ai da mu ka ce mu na neman kasar Yarabawa, to ba wasa mu ke yi ba.

“Dukkan gwamnonin Yarabawa na tare da mu. Daga Oyo, Ogun, da Ondo zuwa Ekiti, duk su na goyon bayan mu. Amma ba za su iya fitowa su furta ba, su na gudun kada a daina turo masu da kudade daga Abuja.

“Saboda haka ku daina zagin gwamnonin mu. Kun ga ai Gwamna Oyetola an sanar da shi zuwa na, kuma ya kyale mu yi taron mu. Sarakunan gargajiyar mu su ma su na tare da mu.”

Yayin da bai bayar da wata shaidar goyon bayan da ya ce gwamnoni ko sarakunan kudu ke ba su ba, ya jaddada cewa zai yi bore ga duk jiga-jigan Yarabawan da su ka ki goyon bayan sa.

Dama kuma an yi irin wannan gangami a Oyo a karshen Afrilu, sai farkon watan Mayu aka yi irin sa a Ogun.

Share.

game da Author