Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya nada wa dakatacciyar Shugabar Hukumar Tashoshin Sufurin Jiragen Ruwa Kwamitin Bincike na mutum 11.
Kwamitin wanda aka nada a ranar Litinin, an dora masa alhakin binciken wasu batutuwa har guda bakwai, tare da duk wasu abubuwan da aka iya cin karo da su a kan hanyar bincike, to a iya yin ribar-kafa da su.
Da ya ke rantsar da kwamitin, Amaechi ya hore su su yi aiki mai kyau, kuma su yi binciken kwakwaf.
Ya ce ba wani bi ta da kulli ba ne ko gadar zare. Ya ce Hukumar NPA a karkashin kulawar ma’aikatar sa ta ke.
“A matsayi na na wanda ma’aikatar da dukkan ma’aikatan cikin ta ke karkashin kulawa ta, to ya kasance tsawon shekaru ban ma san abin da ke faruwa a hukumar tashoshin ruwan ba.
“Kuma daya daga cikin aiki na a matsayin minista shi ne na binciki dukkan ma’aikatu da hukumomin da ke karkashi na..
“Ku ‘yan kwamiti ku yi aiki tukuru. Ku gayyaci duk wanda ku ke so ya warware masu wata mishkila ko da ni ministan ne da kai na. Zan iya zuwa gaban kwamiti na fadi gaskiyar abin da na sani.” Inji shi.
‘Siradin Da Masu Bincike Za Su Dora Hadiza Bala A Kai:
1. Kwamiti zai bincike irin tsare-tsaren da Hadiza Bala ta tafiyar da shugabancin NPA. Sannan su binciko idan bisa ka’ida ta rika tafiyar da aikin ta, tun daga 2016 zuwa ranar da aka dakatar da ita.
2. A binciki dukkan dalilan rushewa da soke wasu kwangiloli da Hadiza Bala ta yi. Sannan a gano shin ,bisa ka’ida ta soke su, ta bi umarnin kotu ko umarnin da Shugaban Kasa ya bayar ne?
3. A binciko ko an rika aiki da ka’idar gudanar da aikin gwamnati a Hukumar NPA, wato idan na kasa na sanar da na sama da shi abin da za a yi, ko wanda aka rigaya aka shi, ko kuma ana yin wanda ys dace a yi tare da shi.
4. A binciko kuma a gano yadda aka rika bayar da keangiloli a karkashin Hadiza Bala tun daga cikin 2016 zuwa ranar da aka dakatar da ita.
5. Kwamiti zai bijoro da shawarwarin yadda za a karfafa ayyukan Hukumar NPA da yadda za a yi wa tufkar da ta warware hanci idan an gyara.
6. A binciki duk wani abu da aka ci karo da shi wanda ke bukatar a yi masa bincike.
7. Binciken kwangiloli zai hada da yadda aka bayar da su, wadanda aka bai wa kwangilolin da kuma yadda aka yi kwangilolin.
Da ta ke magana, Karamar Ministar Ilmi ta ce ta yi mamakin irin yadda mutane ke yi wa lamarin wata birkitacciyar fassara.
Shi ma Shugaban Kwamiti Suleiman Auwalu ya ce za su yi aiki tsakani da Allah ba tare da nuna son kai, son rai ko fifiko ba.
Kuma za su fito da sakamakon da ‘yan Najeriya za su yaba da aikin da su ka yi.
Amaechi ya ce kwamiti ya je ya ci gaba da aiki kawai, ba a ba shi rana ko wa’adin kwanakin kammala binciken sa ba.
Discussion about this post