Babban Kwamandan Sojojin Runduna ta 1 ta Kaduna, Manjo Janar Danjuma Ali-Keffi, ya bayyana alwashi da ƙudirin sojojin ƙasar nan wajen ganin sun kakkabe dukkan wata barazanar tsaro a faɗin Najeriya.
Ali-Keffi ya ce sojojin Najeriya ba za su sake saurarawa ko sararawa ba, har sai sun daƙile matsalolin tsaron ƙasar nan baki ɗaya.
Ya yi wannan bayani ne a matsayin sa na babban baƙo mai jawabi, wurin bikin yaye sabbin kuratan sojoji 6400 da aka yi a Kwalejin Horas da Kuratan Sojoji a Zaria.
Yaye kuratan na wannan shekara dai shi ne na 80, tun bayan kafa kwalejin cikin 1924, babban aikin kwalejin shi ne ta riƙa maida fararen hula sojoji, domin a riƙa cike gurabun dakarun da ake buƙata cikin aikin soja a Najeriya.
“Saboda haka amfanin wannan kwaleji ya na da muhimmanci ƙwarai, musamman a yanzu da ƙalubale daban-daban na tsaro ke fuskantar ƙasar nan.
“Saboda haka daga yau kenan yawa da ƙarfin sojojin Najeriya ya ƙaru da mutum 6,400 da su ka ƙunshi maza da mata.
Ya tunatar wa sojojo rantsuwa d alƙawarin da su ka ɗauka dangane da kama aiki, kuma su kauce wa yin duk wani abin da zai zubar da darajar Sojojin Najeriya da kuma ƙasa baki ɗaya.
A wurin bikin, har harba bindiga sama sau bakwai, domin gaisuwar jinjina ga marigayi Janar Ibrahim Attahiru, da sauran sojoji 10 wadanda su ka mutu tare a hatsarin jirgin sojoji, ranar Juma’a, 21 Ga Mayu.
Discussion about this post