Ban taɓa daukar gwamnan Benuwai da wani mahimmanci ba – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa bai taba daukar gwamnan Benuwai, Emmanuel Ortom da wani mahimmanci ba, domin gazawarsa ba ya misaltuwa, kullum, yana sukar gwamnatin tarayya ne kan gazawarsa.

El-Rufai ya kara da ba da misalin yadda ma’aikatan jihar Benuwai ke bin bashin albashin watanni masu yawa a jihar, bai iya yin komai ba sai dai ya kullum gwamnatin tarayya ta gaza, ta gaza.

” Yana kanannade da matsalolin sa na rashin iya gudanar da al’amurar gwamnati a jihar sa, amma a kullum kukan sa, shine gwamnatin tarayya ta yi wannan, gwamnatin Tarayya kaza.

A karshe El-Rufai ya ce tabbas akwai rashin fsaro da ake dama da shi a fadin kasar nan wand gwamnati tarayya ke sakwa-sakwa da su.

Martanin Ortom

Ortom ta hannun Kakakin sa ya shaida cewa wannan magana da suka karanta bai yi musu dadi ba domin bai kamata ace kamar El-Rufai bane dake da guntun kashi a bayan sa zai fita yana irin wannan magana.

” Na fi karfin El-Rufai ya yi min Izgilanci domin shine abin tausayi, wanda matsalolin da ya kirkiro da hannun sa suka dabaibayeshi ya kasa warware su, ya kyale mutanen kaduna na ta iyo cikin kogin wahala da ra shin zaman lafiya, amma ya na wage baki a inda ba huruminsa bane.

” El-Rufai mai ci da addini ne, domin kowa ya san yadda ya dauki gatari ya datse zaman lafiya dake tsakanin ‘Yan Kaduna aka samu rarrabuwar kai a jihar, kuma ya kasa magance matsaloli da barakar da ya kirkiro su da hannunsa a jihar.

” Kai bari in gaya muku karara ku saurareni, El-Rufai na daga ciki, wadanda suka kai Buhari suka baro a kasar nan. Ba shi da hurumin da wai ace yau El-Rufai ne zai zargi gwamna Ortom na rashin tabuka komai, shi me yayi a Kaduna in banda barusa da raba kan jama’a.

” Kwana-kwanan nan ya kori ma’aikata akalla dubu 4000 a jihar sa. Wannan mutum ne mai tausayi. Bashi da ita.”

Share.

game da Author