Babban Jojin Najeriya ya gana da Ministan Kwadago, ya roki ma’aikatan kotu su janye yajin aiki

0

Babban Jojin Najeriya Tanko Muhammad ya gana da Ministan Kwadago Chris Ngige a ranar Talata, kuma ya yi kira ga Shugabannin Kungiyar Ma’aikatan Kotunan Najeriya (JUSUN) su yi hakuri su janye yajin aikin da su ke yi.

Kakakin Yada Labarai na Babban Jojin Ahuraka Isah ne ya sanar da haka, cikin wata takarda da ya fitar tare da sa mata hannu a madadin Tanko Muhammad.

JUSUN sun fara yajin aikin dakatar da shari’u a dukkan kotunan kasar nan tun a ranar 6 Ga Afrilu, inda su ka sha alwashin cewa ba za a sake zaman kotu ana gudanar da shari’u a kotu ba, har sai gwamnonin kasar nan sun bai wa kotuna da bangaren shari’a ‘yancin cin gashin kan su, kamar yadda sabuwar dokar da Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa hannu ta gindaya cewa a rika yi.

JUSUN ta bukaci kudaden bangaren shari’a da kotuna da ba ma’aikatan kotu da su rika zuwa kai tsaye gare su, ba ta hannun gwamnoni ba.

Zuwa yau dai kwanaki 43 kenan kotunan jihohi da na tarayya duk su na garkame da kwado.

To sai dai kiran da Babban Jojin Najeriya ya yi wa JUSUN, inda ya roki su koma aiki, ya zo ne bayan da Ministan Kwadago, Ngige ya sanar da shi sakamakin ganawar tawagar Gwamnatin Tarayya ta yi da Shugabannin JUSUN, wadda shi Ngige din ne ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya.

“Babban Jojin Najeriya ya damu matuka da tsaikon shari’un da ake fuskanta a kotunan kasar nan. Saboda haka ya na kira ga JUSUN su daure su janye yajin aiki domjn hakan zai amfani kasar nan a da kuma tsarin shari’a.

“Babban Joji na ganin cewa janye yajin aikin za sa a samu zararin magance dambarwar da ake yi cikin ruwan sanyi.”

Ba a sani ba ko JUSUN za su ji rokon da Babban Joji ya yi masu har su janye yajin aiki. Ko kuma shi ma za su watsa masa tayin janye yajin aikin a fuskar sa, kamar yadda JUSUN din ta watsa wa Gwamnonin Najeriya tayin janye yajin aiki a fuskokin su, cikin makon da ya gabata.

Share.

game da Author