Kakakin kungiyar IPOB Emma Powerful ya karyata ‘yan sandan Najeriya cewa da suka yi wai mayakan IPOB ne suka kashe Marigayi Ahmed Gulak a garin Owerri.
Powerfull ya ce babu abinda ya hada kungiyar IPOB da kisan Ahmed Gulak domin ba shi ne a gaban su ba.
” Muna kira ga ‘Yan sanda su je can su nemo asalin wadanda suka kashe Ahmed Gulak, su daina kala wa ‘yan kungiyar IPOB, domin babu abinda ya hada mu da shi kuma, namu da ban, abinda ya kawo shi jihar Imo kuma aka kashe da ban.
Binciken ‘Yan sanda
Bayan kashe fitaccen ɗan siyasa, Ahmed Gulak da wasu ƴan bindiga suka yi a garin Owerri jihar Imo, ƴan sandan jihar sun yi zuga sun bi sawun su kuma sun yi nasarar darkake su.
Ƴan sanda sun ce bayan samun rahoton kisan Gulak, sun bi sawun maharan nan take kuma sun yi nasarar cim musu.
” Mutum shida daga cikin su da wasu huɗu sun ji rauni a jikin su.”
Direban Ahmed Gulak da wani dake tare da shi a a lokacin da suka kashe shi, duk sun tabbatar da waɗanda aka kashe da motocin da suka yi amfani da su.
” Ko da muka bi su zuwa wani gari dake kusa da Owerri, mun iske su suna raba wa kauyawa tulin albasa. Sun yi fashin babbar motar albasa daga Arewa, suka rika raba wa ƙauyawa ganimar albasar, inda mu kuma a daidai muka diran musu.
” Da suka hango mu muna zuwa dabbda su sai suka fara buɗe mana wuta, daganan da yake muma a shirye muke, muka fara maida musa da ruwan albarusai. Duka mutane shidan da suka kashe Gulak mun kama su, wasu sun mutu, wasu kuma ba su mutu ba, amma kama su har da motocin da suka yi amfani da su a lokacin da suka kashe Gulak.
Bayan haka mun kwato bindigogi kirar AK 47 guda uku, karamar bindigar aljihu daya, harsasai 92, da kullin kayan tsaface tsafacen. Sannan sun ɓarnata wasu motocin ƴan sanda da harsashi a lokacin batakashin amma basu lalace ba.
Discussion about this post