Sanata Bala Na’Allah daga Jihar Kebbi ya bukaci dukkan ‘yan Najeriya su tashi tsaye wajen taimakawa a magance maganin tsaro, su daina dora wa Gwamnatin Shugaba Buhari laifin tabarbarewar tsaro a Najeriya.
Na’Allah ya yi wannan jawabi bayan ya fito daga wata ganawa da ya yi da Shugaba Buhari a Fadar Shugaban Kasa, a ranar Lahadi.
Ya shaida wa ‘yan jarida cewa ya kai wa Buhari ziyara domin tattauna wasu muhimman baturuwan da su ka shafi kasar nan.
Ziyarar sanatan ta zo ne kwanaki hudu bayan Majalisar Dattawa ta yi taron sirri na sa’o’i hudu da Shugabannin Bangarorin Tsaro na Kasa.
Kuma ta zo ne bayan da Majalisar Dattawa ta zartas da cewa za ta tura tawagar shugabannin majalisa zuwa ga Shugaban Kasa, domin tattauna gagarimar matsalar tsaro a kasar nan.
Sai dai Na’Allah bai ce ya kai ziyarar a madadin shugabannin Majalisar Dattawa ba.
Ya kara da cewa zaluncin da mu ka rika yi wa junan mu a baya ya haddasa Boko Harama Gabas da kuma ‘yan bindiga a Arewa maso Gabas.
“Kawai dai babban abin takaicin shi ne yadda matsalar ke addabar mu a yanzu zamanin wannan gwamnatin.
Discussion about this post