Jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta maida wa jam’iyyar PDP martani cewa da ta yi wai gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya ciwo bashin da mo jikoki ba za su iya biya ba, kila sai dai ko tattaba kunne, ko kuma uhhuhuh.
Wannan korafi wanda jam’iyyar ta yi ta bakin wani jigo a jam’iyyar, Manjo Yahaya Ibrahim Shunku, a tattaunawa da yayi da BBC Hausa ya ce yan kaduna sun kade, domin El-Rufai ya ciwo jihar bashin da ko jikokin yan Kaduna ba za su iya biyan su ba.
” Lokacin da wannan gwamnati ta APC ta zo a shekara ta 2015, ana bin jihar Kaduna bashin sama da dala miliyan dari biyu da ashirin da shida – kusan gwamnoni 15 kafin zuwan wannan gwamnati.”
Sai dai kuma jam’Iyya mai mulki bata ja bakinta ta tsuke ta yi shiru ba don ko ta maida wa PDP martani.
Sakataren jam’iyyar ya shaida cewa Baba Pate ya ce” Namu ba irin na su bane. ”
” Ai mu bashin da muke ciyowa ba irin bashin da gwamnatocin baya ke karbowa bane. Mu namu dai na farko wasu ma ba ruwa a ciki, tsurar kudin da ka amsa shi ne za aka biya. Sannan wasu basukan za a rika biya kadan-kadan ne ba bu takura.
“Abokin hamayya ai kullum ba zai yi maka adalci ba’ saboda mutanen jihar sun san cewa gwamnati ta ciyo bashin domin ci gaban al’umma ne. ba magana ba ce da mai hankali zai ɗauka, a gwamnatinmu muna da masana da suke ba gwamnati shawara kan ko mene gwamnati za ta shiga”.
Sannan kuma ya ce su kan su mutanen Kadyna sun shaida kuma suna ganin kudin da aka ciwo bashin su ana musu aiki da su.