• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Buhari Travelling

    Duk da tsananin hare-haren da ya darkaki Najeriya a kwanakin nan Buhari zai waske taro Dakar

    An cika sansani uku fal da tubabbun ‘yan Boko Haram -Gwamna Zulum

    RUƊANI A APC: Gwamnan Neja, Bello ya ɗare kujerar Buni, Buhari ya bada umarnin Buni ya sauka daga shugabancin jam’iyyar

    IHU BAYAN HARIN SHIRORO: Gwamnatin Neja ta dakatar da haƙar ma’adinai a Shiroro, Munya da Rafi

    Barayi sun lalata tiransifoma 20 cikin makonni uku – Kamfanin Raba Wutar Lantarki

    SADAKA GUZURIN KIYAMA: Tsohon gwamnan da ya taya akanta jidar naira biliyan 84, ya yi wa malamai da ‘yan APC watandar shanu 370, ragunan layya 3,500 a Zamfara

    ZAƁEN GWAMNAN ANAMBRA: INEC za ta raba kayan aiki marasa hatsari daga Owerri

    ZAƁEN GWAMNAN OSUN: Matsalar tsaro da guguwar sayen ƙuri’u ne abin da ya fi damun mu -INEC

    Ƴan sanda sun ceto ƙananan yara 50 da aka kulle cikin kurkukun wani coci a ƙarƙashin ƙasa, a Ondo

    ‘Na sadaukar da rayuwa ta ga Najeriya’ – Inji sojan da mahara su ka kashe a harin Shiroro

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    LMC ta ci tarar Kano Pillars, ta kori shugabanta, Jambul bayan ya gobza wa ‘Rafiri’ naushi a haɓa

    Inganta Rayuwar Matasa Ta Hanyar Wasan Kwallon Kafa Da Gudunmawar Al’Ummah A Jigawa, Ahmed Ilallah

    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

No Result
View All Result

ANA MUZURU ANA SHAHO: Hare-hare kan ofisoshin INEC ba su hana hukumar fito da tsarin aiki da sabon injin rajista ba

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
May 27, 2021
in Manyan Labarai
0
Yawan hare-hare kan ofisoshin INEC zai iya kawo wa zabukan 2023 cikas -Farfesa Yakubu

Yayin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tsinci kan ta cikin halin kai wa ofisoshin ta na jihohi da ƙananan hukumomi hare-hare a kudancin ƙasar nan, a daidai lokacin ne kuma ayyuka ke ƙara bijiro wa hukumar, musamman na tsare-tsaren gyaran matakan zaben 2023 da kuma wasu zaɓukan na cike gurabu, sai kuma zaɓe mai zuwa na Gwamnan Jihar Anambra.

A cikin wannan yanayi ake ta kai wa ofisoshin INEC hare-hare tare da banka masu wuta.Har ta kai a farkon makon jiya Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya yi taron gaggawa da Kwamishinonin Zaɓe na Tarayya da ke jihohin ƙasar nan baki ɗaya.

Baya ga banka wa ofisoshin INEC guda shida wuta da aka yi a garuruwa daban-daban a yankin Kudu maso Kudu cikin makonni uku a baya, a makon nan kuma lamarin ya ƙara muni, har ta kai Shugaban INEC ya ce hare-haren da ake kai wa za su iya kawo cikas a zaɓen gwamnan Jihar Anambra.

Kwanaki biyu da su ka gabata an banka wa cibiyar tattara sakamakon zaɓe wuta a Jihar Anambra.

Haka nan kuma an sake banka wa wani ofishin INEC wuta a Enugu, yayin da kuma aka kama wasu mutane 37 bisa zargjn su da ake yi su na ƙulle-ƙullen shirin banka wa ofisoshin INEC da na ‘yan sanda wuta.

To sai dai kuma duk da waɗannan hare-hare, INEC ba ta ba yi tsaye wuri ɗaya ta zura ido ba, ta na ci gaba da gudanarwa da aiwatar da ayyukan da su ka shafi zaɓe a ƙasar nan.

A farkon wannan makon Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta yanke shawarar yin aiki da na’urar rajistar masu zaɓe ta zamani ne wajen aikin rajistar masu zaɓe saboda zurfafa aiki da fasahar zamani a tsarin.

Babban kwamishina kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe da yaɗa labarai a INEC, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a lokacin wata tattaunawa da ya yi da Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) a ranar Litinin a Abuja.

Ya bayyana cewa na’urorin, mai suna ‘Voter Enrolment Device’ (VED), wadda an ƙirƙire ta bisa tsarin ‘android’ na ƙaramar komfuta ta ‘tablet’, za a kawo su ƙasar nan a ranar Litinin, 31 ga Mayu, domin a soma aiki da su a wajen rajistar masu zaɓe a ranar 28 ga Yuni.

Okoye ya ce Hukumar Zaɓe ta daina aiki da tsohuwar na’urar nan mai suna ‘Direct Data Capture Machine’ (DDCM) wadda aka yi aiki da ita a ayyukan rajista da aka yi a baya, kuma yanzu za a maye gurbin ta da sabuwar na’urar.

Ya ƙara da cewa na’urar ta VED za ta bada damarmaki da dama, waɗanda su ka haɗa da kyakkyawar hanyar gane fuskar mutum da zanen hannun mutum kai-tsaye.

Babban kwamishinan ya ce wasu damarmakin kuma su ne daɗin ɗauka da sarrafawa, da kuma “daidaituwa da buƙatun Katin Shaidar Ɗan Ƙasa.”

Ya ce, “Na’urar VED ta bambanta da ta DDC, domin babban ƙullutun aikin DDCM, wato komfutar laptop, an maye gurbin ta da ƙaramar komfutar ‘tablet’.

“Na’urar ta fi daɗin ɗauka fiye da ta DDCM. Na’ura ce ta zamani saboda ɓangarorin ta an yi su ne da fasahohin da aka inganta tare da sabunta su fiye da na DDCM.

“A yanzu da lokacin fara aikin ya ƙarato, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, zai yi wa mutanen ƙasar nan ƙarin bayani kan hanyoyin da aka tsara na fara aikin da kuma yawan cibiyoyin da aka tanadar wa ‘yan Najeriya.’’

Okoye ya ce saboda kiyayewa da sashe na 10(2) na Dokar Zaɓe ta 2010 (wadda aka gyara), INEC za ta yi amfani da hanyar gamin gambiza ta aikin rajista ido da ido da kuma ta yanar gizo.

Ya ce, “‘Yan Najeriya waɗanda ba su iya komfuta ba ko waɗanda ke zaune a yankunan karkara za su iya fara rajistar su har su gama a kowace daga cikin cibiyoyin rajista da aka tanadar.

“Waɗanda ke da komfuta ko ‘tablet’ ko babbar wayar hannu za su iya fara yin rajistar su ta hanyar yanar gizo kuma su kammala shigar da bayanan su a kowace daga cikin cibiyoyin da aka ware.

“Gidan yanar zai kasance ya na da ɓangaren yin rajista da alamar da ke nuna wurin yin zaɓe waɗanda za su taimaka wa masu yin rajista wajen sanin wurin da za su yi rajista da wurin yin zaɓe mafi kusa da su.”

Karanta kuma Shugaban INEC na so jama’a su kare kayan hukumar daga masu ƙona su Okoye ya ce Yakubu zai bayyana wa ‘yan Najeriya yawan rumfunan zaɓe da na wuraren yin zaɓe na unguwa waɗanda aka mayar cikakken rumfunan zaɓe masu zaman kan su, da jimillar rumfunan zaɓe da ake da su a duk Najeriya.

“INEC ta karya ƙwarin wata matsala da ta shafe shekaru 25 ana fama da ita wadda ta danganci ƙara yawan rumfunan zaɓe, kuma ‘yan Nijeriya za su samu damar sababbin rumfunan zaɓe.

“Rumfunan zaɓen za su bada dama ga naƙasassu da mata masu ciki da tsofaffi su samu damar yin zaɓe ba tare da wata wahala ba.

“Irin waɗannan rumfunan zaɓen za su kasance masu sauƙin isa gare su, da kuma sauƙin sarrafawa. Za su samar da damar yin tazara da juna kuma za su ba ma’aikatan mu na wucin gadi damar yin aikin da doka ta rataya masu a wuya cikin sauƙi.’’

Okoye ya ce rajistar masu zaɓe babban ginshiƙin tsarin dimokiraɗiyya ne, domin za ta ba ‘yan Nijeriya waɗanda su ka kai shekarun da kundin tsarin mulki ya amince masu da su yi rajista su yi amfani da ‘yancin su na dimokiraɗiyya.

Karanta kuma Za a yi Babban Zaɓen 2023 a ranar 18 ga Fabrairu – INEC

“Saboda haka, ‘yan Najeriya da su ka kai wannan zango na tsarin mulki da dokar ƙasa na yin rajista za su samu damar yin rajista.’’

Ya ce a taron da ya yi da manema labarai a ranar 1 ga Afrilu, Yakubu ya faɗi cewa rajistar masu zaɓe wata dama ce ga dukkan ‘yan Nijeriya waɗanda su ka kai shekara 18 da haihuwa kuma ba su taɓa yin rajistar yin zame ba.

Jami’in hukumar ya ce za kuma a bada dama ga kowane mai rajista wanda ke da wani kuka a lokacin ɗaukar bayanai a zaɓuɓɓukan da aka yi a baya, saboda hukumar ta gyara duk wata matsala.

Ya ce, “Dukkan masu zaɓe da aka yi wa rajista waɗanda ke so su sauya wurin jefa ƙuri’ar su zuwa wani wajen; da masu zaɓe da aka yi wa rajista waɗanda su ka ɓatar da katin su na zaɓe (PVCs) ko waɗanda katin su ya lalace, duk za a ba su dama.

“Haka su ma dukkan masu zaɓe da ke da rajista waɗanda ke so su yi gyara kan bayanan su kamar rashin rubuta suna a daidai ko kwanan watan haihuwa, da sauran su.”

Previous Post

Buba Galadima ya karyata zargin ya na zawarcin PDP, ya ce rAPC za ta dawo ta girgiza siyasar Najeriya

Next Post

WALLE-WALLE DA KUƊAƊEN SATA: Minista Malami ya ce bai yi wa Najeriya sagegeduwar ƙwato daloli biliyan 60 daga Amurka ba

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • KOWA TA SA TA FISSHE SHI: Ƙoƙarin haɗewar LP da NNPP ya kakare, Peter Obi zai bayyana mataimakin takarar sa ranar Juma’a
  • ‘Da gangar aka bari ƴan bindiga suka kai harin gidan yarin Kuje, saboda na yi ta faɗin hakan zai auku – Mamu
  • Ƴan bindiga sun babbake cibiyoyin kiwon lafiya sun yi dalilin dole aka rufe wasu 69 a Katsina
  • Dala ta ƙara kekketa wa naira rigar mutunci daidai lokacin tsadar kayan abinci
  • Duk da tsananin hare-haren da ya darkaki Najeriya a kwanakin nan Buhari zai waske taro Dakar

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.