An yi gumurzu tsakanin sojoji da Boko Haram din da su ka hana mazauna Maiduguri yin buda-baki cikin natsuwa

0

Sojojin Najeriya sun fatattaki Boko Haram a wani farmaki da ‘yan ta’adda din su ka kai a unguwar Jiddare Filin Polo, a Maiduguri da yammacin ranar Talata.

An fara bude wuta tun wajen karfe shida na yamma har karfe bakwai a lokacin buda-baki.

Mazauna unguwar sun rika tururuwa a guje su na tserewa cikin Maiduguri a lokacin da ake gwabza artabun.

An rika jin rugugin karar manyan bindigogin atilare na tashi, kuma an rika ganin motocin sojoji a sukwane su na tunkarar unguwar tare da motar sojoji mai daukar marasa lafiya.

Wani soja daga Bataliya ta 7 ya tabbatar da faruwar lamarin ta wata amsar tambayar jin ba’asi da ya bayar ta sakon ‘tes’.

Wannan ne hari na farko da Boko Haram su ka kai Maiduguri tun farkon azumi tsawon kwanaki 29.

Har zuwa yanzu dai ba a san yawan wadanda aka jikkata ko aka kashe a bangaren sojoji ko ‘yan ta’adda ba.

Share.

game da Author