An kashe mutum 323, an yi garkuwa da mutum 949 cikin watanni uku a jihar Kaduna – Rahoto

0

Bayanai kan tsaro da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar ranar Juma’a sun nuna an kashe mutum 323 kuma an yi garkuwa da mutum 949 a cikin watanni uku a jihar.

Yankin Kaduna ta Arewa ke da karancin yawan mutanen da aka kashe da yawan mutanen da aka yi garkuwa da su.

Daga cikin mutum 323 din da aka kashe a jihar an kashe mutum kashi 73.07% a Yankin Kaduna ta Tsakiya, mutum kashi 21.05% a Kaduna ta Kudu da mutum kashi 5.88% a mazabar Kaduna ta Arewa.

Sannan daga cikin mutum 949 din da aka yi garkuwa da su a jihar an yi garkuwa da mutum kashi 82.4% a mazabar Kaduna ta tsakiya, mutum kashi 13.59% a mazabar Kaduna ta Kudu da mutum kashi 4% a mazabar Kaduna ta Arewa.

An kashe mahara 164 a jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaro Da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa rundunar sojin Najeriya ta kashe mahara 64 sannan rundunar sojoji Sama ta kashe mahara 100.

“Daga cikin mutum 323 da aka kashe akwai mata 20, yara kanana 11 da maza 292.

“An kashe mutum 236 a kananan hukumomin Birnin Gwari, Chikun, Igabi, Giwa da Kajuru.

“Birnin Gwari garin da ya fi samun yawan mutanen da aka kashe a jihar na da mutum 77.

“An kashe mutum 52 a Chikun with 52, Igabi 45, Giwa 42, Kajuru 20 duk a tsakanin watanni uku.

“An kashe mutu 68 a Kudancin Kaduna inda daga ciki akwai mata 5 da yara 18.

“An kashe mutum 28 a Kajuru, mutum 14 a Zangon Kataf da mutum 12 a Kagarko.

“An kashe mutum 19 a Arewacin Kaduna inda Zaria ce garin da ta fi samun yawan mutanen da aka kashe da mutum 6.

Bayan haka Aruwan ya ce an kwace bindigogi kiran AK47 36 da harsasai 1959.

Ya ce jami’an tsaro za ta ci gaba da gudanar da bincike domin ganin ta kamo wadanda ke safarar bindigogi zuwa jihar.

Share.

game da Author