An kai wa ofisoshin INEC hari sau 41 cikin shekara biyu -Farfesa Yakubu

0

Shugaban Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa an kai wa ofisoshin hukumar hare-hare har sau 41 a cikin shekaru biyu.

Yakubu ya bayyana haka ne a wurin wani taron gaggawa da ya gudana tsakanin INEC da bangarorin jami’an tsaro, a Abuja.

Ya ce daga yanzu za a ɗauki hare-haren da ake kai wa ofisoshin INEC a matsayin wata babbar matsalar tsaro a ƙasar nan.

Ya ce yawan hare-haren da masu banka wa ofisoshin zabe wuta ke kaiwa, sun zama babbar barazana ga ayyukan da hukumar ke tsarawa, musamman waɗanda zu ka danganci tsare-tsaren zabe.

“A cikin shekaru biyu ɗin nan, an kai wa ofisoshin INEC hare-hare sau 42. A ciki, an kai hare-hare sau tara a cikin 2019, cikin 2020 kuma sau 21.

“A cikin makonni huɗu da su ka shuɗe, an kai hari kan ofisoshin INEC sau 11. Wasu ofisoshin wuta aka banka masu, wasu kuma kutsawa aka yi aka saci kaya kuma aka lalata wasu. Biyu daga cikin waɗannan hare-haren kuwa Boko Haram ne su ka kai su da kuma ‘yan bindiga. Sai kuma batagari da ‘yan iskan gari sun kai na su hare-haren sau 10 a lokutan zabe da kuma bayan kammala zabe.

“Sai dai kuma hare-hare 29 cikin 41 ɗin da aka kai, ba su ma da wata alaƙa da zabe ko ayyukan da su ka danganci jefa ƙuri’u.

“Wato 18 cikin hare-haren sun faru ne lokacin tarzomar #EndSARS da aka cikin Oktoba, 200. Sauran hare-hare 11 kuwa duk batagari ne su ka kai su, sai kuma ‘yan bindigar da ba a san ko su wane ba.”

Asarar Da INEC Ta Yi Sanadiyyar Hare-hare A Ofisoshin Ta:

Shugaban INEC ya ce duk da dai hukumar ba ta kammala ƙididdige yawan asara ko kayayyakin da aka lalata ba, amma binciken farko ya nuna cewa a cikin kayan da aka lalata wa INEC, akwai: akwatin zabe 1,105, rumfar zabe 694, janareto 429 da kuma motoci ƙirar Toyota Hilux guda 13.

Yakubu ya nuna cewa akwai tabbaci da yaƙinin cewa idan aka ƙara samun haɗin kai da bangarorin jami’an tsaro, to za a iya magance wadannan hare-hare.

Ya ce a baya hare-hare ne ɗaiɗaiku ake kai wa INEC, amma yanzu salon ya canja, sai masu kai hare-haren sun yi shiri, sun tsara irin barnar da za su yi. Sannan kuma a yanzu maharan tantagaryar batagari ne da su ka ɗauko hanyar kawo wa ayyukan INEC cikas gadan-gadan.

Da ya ke jawabi, Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Tsaro, Babagana Monguno, wanda kuma shi ne Shugaba na 2 na Kwamitin Tattauna Batutuwan Tsaron INEC (ICCES), ya ce ofishin sa na aiki tare da sauran bangarorin tsaro domin tabbatar da ganin dimokraɗiyya ta ɗore a ƙasar nan.

Monguno ya ce za a kawo karshen waɗannan hare-hare da tashe-tashen hankula a ƙasa baki ɗaya.

Shi ma Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Usman Baba, ya sha alwashin cewa jami’an ‘yan sanda za su zage damtsen ganin an kawar da wannan matsala.

Ya ce duk wasu al’amurra da su ka shafi zabe, ba za su yi nasara ba sai an samar da tsari.

Share.

game da Author