Biyo bayan yawan hare-haren da kisan da ‘yan bindiga ke ta yi wa jami’an ‘yan sanda a Yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Delta ta yi kakausan gargadi ga jami’an ta cewa su gaugauta dakatar da yin rakiyar kariyar tsaron lafiya ga manyan masu mulki ko jami’an gwamnati zuwa wasu jihohin kudu shida.
Jihohin da sanarwar ta shafa sun hada da Abia, Anambra, Enugu, Ebonyi, Imo da kuma Ribas da ke yankin Kudu maso Kudu.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Delta ne ya bayyana wannan sanarwa a Asaba, babban birnin jihar Asaba.
Sakon wanda ya sanar ta sakon nan-take na “wireless”, ya tura shi ga Gidan Gwamnatin Jihar Delta, Majalisar Dokokin Delta, Hukumar Raya Yankin Hako Man Fetur ta Jihar Delta, NNPC a Ofishin Delta da wasu wurare.
Haka kuma an gargadi ‘yan sanda kada su kuskura su kara raka wani jami’i ko mai mulki ko dan siyasa a wadannan jihohi, har sai komai ya daidaita an ba su umarni tukunna.
PREMIUM TIMES HAUSA ta rika bada labarin yadda ‘yan bindiga ke bin jami’an tsaro su na kashewa, tare da kone ofisoshin su a wadannan jihohi.