An gabatar da Shahadar Khalifanci ga Mai Martaba Khalifah Sarki Malam Muhammadu Sanusi II

0

Jagorar darikar Tijjaniya na Duniya ya mika wa sarki Sanusi II shahadar Khalifanci.

Khalifa Sanusi Lamido II yanzu shine jagoran darikar Tijjaniya kuma Khalifan Sheikh Ibrahim Inyas ya Najeriya.

Shugaban darikar Tijjaniya duniya, sheikh Mahi Niass, ya tabbatar wa sarki Sanusi II khalifancin darikar Tijjaniya na Najeriya baki daya.

Sheikh Inyass ya gayyaci Sarki Sanusi shan ruwa a garin Kaolack, kasar Senegal, in da a nan ne ya jaddawa sarki Sanusi wannan shugabancin da aka yi masa na jagorar darikar Tijjaniya a Najeriya.

Idan ba a manta ba, wakilin Sheikh Inyas, ya sanar da nadin Sarki Sanusi sabon Khalifan Tijjaniya a Najeriya wanda ya gaji marigayi, Isiyaka Rabiu a garin Sokoton Najeriya a taron Maulidi da darikar ta yi.

Sai dai bayan wannan taro, ‘yan bangaren sheikh Dahiru Bauchi, suka ki amincewa da wannan nadi, inda daya daga cikin’ ya’yan sa Ibrahim Nahiru Bauchi, ya karyata nadin yana mai cewa, ba a yi haka ba.

Niass ya hori sabon Khalifan ya rike mutane da adalci kamar yadda yake a addinin musulunci.

Share.

game da Author