AN FARA SHATA LAYI: Bukatun Da Gwamnonin Kudu 17 Ke Nema 12

0

1. Mu Gwamnonin Kudu 17 mu na kara jaddada bukatar ganin cewa Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya dunkulalliya, amma a bisa turbar adalci ga kowane bangare na yankin kasar nan baki daya.

2. Mun lura cewa kwararar makiyaya masu dauke da muggan makamai da sauran manyan masu laifuka zuwa cikin yankin Kudanci, lamarin na kara nuna irin matsalar tsaron da ta kai jama’a su na zaune cikin halin kasa gudanar da rayuwar su da ta hada da kasuwanci da harkokin noma da bunkasa tattalin arziki. Wannan kuwa ya haifar da barazana ga samar da abinci da kuma barazana ga tsaro baki daya.

To dalilin haka mun hana kiwo kwata-kwata a jihohin kudu. Wato kiwon da ba a iya daure dabbobi a ciyar da su, sai dai a rika gararambar yawo da su ana neman abinci.

3. Mun hana yawon kiwo ana karkado dabbobi daga Arewacin kasar nan ana nauso mana da su nan Kudu.

4. Mun goyi bayan Gwamnatin Tarayya cewa ta fito ta taimaka wa duk jihar da ta ga za ta yi tsarin kiwon dabbobi na zamani.

Don haka mu na bukatar a gaggauta sauya fasalin Najeriya ta yadda za a amince kowace jiha ta kafa ‘yan sanda na kan ta. Kuma a sake fasalin rabon arzikin kasa, a sake fasalin rabon kudaden shiga ta yadda tsarin zai fifita jihohin da aka fi samo arzikin daga yankunan su. Wannan shi ne zaman gaskiya, babu cuta ba cutarwa na tsarin federaliyya ta zahiri.

5. Mu na sanar da cewa saboda masu tayar da jijiyoyin wuya a kasan, mu na kira da a gaggauta kiran taro na kasa.

6 Akwai bukatar a sake duba irin yadda aka yi nade-naden mukamai yanzu haka a Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatin Tarayya, ciki kuwa har da Hukumomin Gwamnati.

7. Mu Gwamnonin Kudancin Najeriya na kira ga gaggawa a kira Babban Taron Tattaunawa na Kasa, ganin yadda bangarorin kasar nan ke ta karajin korafe-korafen neman a rika tafiya tare da kowane sashi a tafiyar da gwamnati.

8. Mun zartas cewa akwai bukatar mu kara dankon zumunci da hadin kai tsakanin Jihohin Kudu da kasar nan baki daya.

9. Mun matukar damu da yadda ake samun matsanancin cinkoson motoci a kan babban titin Apapa, tashar ruwan da can ne jijiyar tattalin arzikin Najeriya. Wannan cinkoso na kawo koma baya sosai ga tattalin arziki.

Saboda haka mun zartas da cewa Gwamnatin Tarayya ta gina karin tashoshin jirage a wasu jihohi domin saukake wancan cinkoso na Tashar Apapa.

10. Mun damu da kokarin sake kulle kasar nan saboda korona. Saboda kullewar za ta haifar da matsananciyar matsalar tattalin arziki. Saboda haka mu na kira Gwamnatin Tarayya ta hada karfi da Gwamnatocin Jihohi domin a bijiro da hanyar dakile cutar korona ta bai-daya.

11. Mu na matukar damuwa da gagarimar matsalar tsaro da ke ci gaba da dagulewa a kasar nan. Ya kamata Shugaban Kasa ya yi wa jama’ar kasar nan jawabin da zai kara wa mutanen kasar nan kwarin guiwa.

12. Mu na matukar godiya ga Gwamna Ifeanyi Okowa saboda daukar nauyin wannan taro da ya yi da kuma karimcin da ya nuna mana yayin taron.

Share.

game da Author