Cibiyar kula da mutanen da aka ci zarafin su dake jihar Enugu ‘Tamar Sexual Assault Referral Centre (Tamar SARC)’ ta bayyana cewa ta saurari kararrakin fyade 25 a tsakanin watanni uku da suka gabata a jihar.
Shugaban cibiyar Evelyn Onah ta fadi haka da take hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN.
Evelyn ta ce a tsakanin wannan lokaci kuma cibiyar ta saurari kararrakin zargin aikata fyade 31 sannan an ci zarafin mata biyar a jihar.
Ta ce wadanda aka yi wa fyaden ba su wuci shekaru 5, 22 da 24 ba.
Bayan haka Evelyn ta ce daga cikin kararrakin da cibiyar ta saurara ta samu labarin yadda wani matashi mai shekara 22 ya yi wa tsohuwa mai shekaru 88 fyade a Nsukka.
Ta ce an ‘yan sanda sun dsmke matashin kuma yana tsare a ofishinsu.
“Mun kuma samu labarin yadda wani ya yi wa mace mai shekaru 47 fyade yayin da take hanyar dawowa daga coci da dare.
“Bayan haka an damke wasu gungun maza da suka yi taron dangi kan wata yar shekara 22, suka ci zarafin ta da karfin tsiya, haka kuma an damke wani saurayi da ya yi lalata da ‘yar shekara 14 da karfin tsiya a hanyar ta ta zuwa rafi debo ruwa.
“Duk an kama mazajen da suka aikata wannan aika-aika, yanzu suna tsare a hannun hukuma.
Evelyn ta ce zaman kashe wando da talauci na daga cikin matsalolin dake kara hassasa fyade da ake fama da shi a jihar.
Ta yi kira ga matasa da su nemi aikin yi su nemi sana’a, su dai na zaman banza. Sannan kuma wadanda aka ci zarafun su su rika kai kara don a bi musu hakkin su.
Cibiyar Tamar Sexual Assault Referral Centre (Tamar SARC) cibiya ce da gwamnati da asusun USAID suka kafa domin yaki da cin zarafin mutane a jihar.
Cibiyar na kula da mutanen da aka ci zarafinsu kyauta a jihar.