Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana cewa binken sirri da jami’an tsaro na sirri da gwamnati ta suka yi ya bayyana wasu gaggan gwamnati, da wasu attajiran kasarnan da ke da hannu dumu-dumu wajen daukar nauyi ‘yan ta’ adda da ta’addanci a kasar nan.
Da ya ke zantawa da manema labarai a fadar gwamnati, Malami ya bayyana cewa gwamnati na nan ta na daukar sunayen su daya bayan daya domin fara bincike akan su da kuma tuhumar su.
” Gwamnati ta tsananta bincike akan wadannan mutane ne bayan kama wasu manyan ‘yan Najeriya da hannu wajen daukar nauyin ta’addanci a kasar, suna dankarawa ‘yan bindiga makudan kudade don gudanar da ayyukan su da ak yi a kasar Dubai.
Bayan hukuncin da kasar Dubai ta yanke akan wasu manyan ‘Yan Najeriya da aka kama suna harkalla da ‘yan kungiyar Boko Haram ta hanyar kashe musu kudade don gudanar da ayyukan hare-hare da suke yi a kasar nan Najeriya ta fara bin sawun ire-ren wadannan mutane.
” Ina so in sanar muku cewa an gano wasu manyan ‘yan Najeriya gagga-gagga gami da manyan ‘yan kasuwa dake jika Boko Haram da mara wa ‘yan ta’adda da kudade masu yawa. Wannan ba zato, zargi ko hauragiya bane, an tabbatar da su da kwararan hujjojin da ya tona asirin su.
” Kuma wadannan mutane sun fito ne daga sassan kasar nan, kudu, Arewa, duka. Zuwa yanzu an yi nisa matuka wajen gano ko su waye domin a tarkato su gaba daya a bayyana wa ‘yan Najeriya ta hanyar gurfanar da su.
Discussion about this post