Kasar Amurka bayyana cewa tun bayan bullar annobar Korona ta tallafa wa Najeriya da sama da dala miliyan 73.
Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya bayyana cewa daga watan Maris zuwa Afrilu an yi wa mutum 1,175,285 allurar rigakafin korona a kasar nan.
Hakan ya nuna cewa an yiwa kashi 58.4% na adadin yawan mutanen da ya kamata a yi wa rigakafin a kasar nan.
Ya ce a yanzu haka jami’an lafiya na nan na ci gaba da yi wa mutane allurar rigakafin a duk jihohin kasar nan.
Shu’aib ya koka kan yadda a ke fama da karancin maganin rigakafin cutar yanzu a duniya wanda hakan zai iya kawo cikas musamman ga kasashe masu tasowa.
Ya ce domin gudun kada maganin ya Kare kar-kaf ya sa gwamnati ta dakatar da yi wa mutane allurar rigakafin.
Gwamnati ta umurci jami’an lafiya da su yi wa masu shekaru 18 zuwa sama allurar rigakafin korona a kasar nan.
Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutum 37 da suka kamu da cutar korona ranar Lahadi.
Hukumar ta ce an gano wadannan mutane a jihohi bakwai a kasar nan.
Wadannan jihohi sun hada da Yobe-13, Lagos-12, Akwa Ibom-6, FCT-3, Edo-1, Kaduna-1 da Ogun-1.
Hukumar ta ce babu wanda ya mutu a dalilin kamuwa da cutar a kasar nan.
Zuwa yanzu mutum 165,419 ne suka kamu, mutum 7,054 na killace a asibitocin kula da masu fama da cutar.
Sannan mutum 156,300 sun warke, mutum 2,065 sun mutu a kasar nan.
Discussion about this post