Masarautar Katsina ta tsige Hakimin Kankara, Yusuf Lawal, sakamakon samun da aka yi ya na mu’amala da ‘yan bindiga.
Karamar Hukumar Kankara can ne ‘yan bindiga su ka saci daliban sakandare sama da 300 a lokaci guda.
Sakataren Majalisar Masarautar Katsina, Bello Ifo ne ya shaida wa manema labarai sanarwar tsige hakimin na Kankara.
Ya ce kwamitin da aka nada ya binciki ko hakimin na hada baki da ‘yan bindiga, ya same shi da hannu dumu-dumu wajen mu’amala da su.
Sai dai kuma Sakataren na Majalisar Masarautar Katsina din bai yi wa manema labarai irin hannun da hakimin ke da shi wajen yin garkuwa da mutane ko hare-haren ‘yan bindigar ba.
A ranar 1 Mayu Premium Times ta buga labarin cewa an kafa wa tsigaggen hakimin kwamitin binciken zargin sa da hannu wajen goyon bayan ‘yan bindiga, kuma aka dakatar da shi.
Idan za a iya tunawa, gogarman ‘yan bindigar da su ka sace daliban Kankara, wato Auwalun Daudawa ya tuba daga garkuwa har gwamnatin Jihar Zamfara ta ba shi wurin zama a gefen garin Gusau, babban birnin jihar.
Sai dai kuma ‘yan bindiga sun kashe shi, kwana biyu bayan ya tada tubar sa, ya koma daji.
Discussion about this post