Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris, ya bayyana cewa gaskiya Gwamnatin Tarayya ba ta kai ga maida wa Jihar Delta fam miliyan 4.2 da shi da kan sa ya bayyana wa Majalisar Tarayya cewa an mayar ba.
A ranar Talata ce Idris ya shaida wa Majalisar Tarayya cewa an maida wa Jihar Delta kuɗin jihar da tsohon gwamna James Ibori ya sace, ya kimshe a Birtaniya.
Washegari kuma Gwamnatin Jihar Delta a ranar Laraba ta fito ta ce ƙarya Akanta Janar ya kantara, jihar ba ta karbi ko sisi ba.
‘Akanta Ya Kantara Ƙarya, Ba Mu Karbi Ko Sisi Ba’ -Jihar Delta
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga martanin Jihar Delta, inda ta ce ƙarya Akanta Janar ya kantara, ko sisi ba a bai wa Jihar Delta daga kuɗaɗen satar Ibori da aka karbo ba.
Gwamnatin Jihar Delta ta karyata labari da iƙirarin cewa Gwamnatin Tarayya ta damƙa mata dala miliyan 4.2 na kuɗaɗen satar tsohon gwamnan jihar, James Ibori, waɗanda Birtaniya ta maido wa Najeriya kwaan nan, bayan ta ƙwace su daga hannun James Ibori.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris ya bayyana wa Kwamitin Binciken Kuɗaɗen Sata cewa an maida kuɗaɗen ga Gwamnatin Jihar Delta.
Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Ifeanyi Okowa, Olisa Ifeajika, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa har zuwa ranar ko sisin kwabo bai shiga aljihun jihar Delta da sunan kuɗaɗen satar Ibori ba.
Ifeanyi kuma ya aiko wa PREMIUM TIMES da wasiƙa a ranar, inda ya ƙara jaddada matsayar Gwamnatin Jihar Delta cewa tabbas ba ta kai ga karbar ko sisi ba tukunna.
Sanarwar ta nuna cewa har yanzu Gwamnatin Jihar Delta na tunrubar Ofishin Ministan Shari’a Abubakar Malami domin ganin cewa ta karbi kuɗaɗen.
Sanarwar ta kuma shaida wa ɗaukacin al’ummar Jihar Delta cewa Gwamnatin Ifeanyi Okowa za ta yi amfani da kuɗaɗen ta hanyoyin da su ka dace domin samar da ayyukan inganta rayuwa a jihar Delta.
Ta kuma gode wa Gwamnatin Tarayya a ƙoƙarin ta na ganin an maida kuɗaɗen a inda aka sace su, wato jihar Delta.
Sai dai kuma sanarwar ta ce har zuwa Laraba ba a damƙa wa Jihar Delta kuɗaɗen ba.
‘Gaskiya Ba Mu Kai Ga Bai Wa Jihar Delta Kuɗaɗen Ba -Akanta Janar
A ranar Alhamis kuma kwana ɗaya bayan Jihar Delta ta ƙaryata shi, Ahmed Idris ya fito ya ce gaskiya ba a kai ga bayar da kuɗaɗen ba, amma ana nan ana ‘yan cike-ciken fom da kai-kawon ganin an daddale komai an damƙa wa Jihar Delta kuɗaɗen.
Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Akanta Janar, Henshaw Oguibike, shi ya sanar cewa ana nan ana tsare-tsare da kai-kawon daddale komai.
“Amma dai a gaskiya har zuwa yanzu ɗin nan, ba a kai ga bayar da kuɗaɗen ga Jihar Delta ba.”
Discussion about this post