Ahmed Isah ya roki ‘yan Najeriya su yi hakuri, gaura wa wanda ta babbake kan yarinya mari da yayi

0

Ahmed Isa ya roki ‘yan Najeriya su yi hakuri, gaggaura wa wata mata mari da yayi bayan ta zo shirin sa da ya saba yi kullum a radiyo da talbijin, a dalikin babbake kan wata yarinya.

Ahmed cikin fushi, ya rika gaggaura mata mari bayan ta ki bada bayanai masu gamsarwa game da mummunar abinda da ta aikata na banka wa yar yarin wuta akai babu gaira babu dalili.

Ya ce yayi kuskure matuka marin da yayi mata, amma ya na rokon ayi hakuri.

Akarshe yayi barazanar dakatar da shirin da yake yi, cewa ana yi masa bita da kulli.

Sai dai kuma daga baya hakan bai karbu ba daga masu kallo da saurare ba domin mutane sun roke shi ya hakura ya janye wannan shawara.

Martanin jama’a

A cikin wannan mako ne aka fitar da wani bidiyo da ke nuna bajinta da ayyukan alkhairi da mai gidan talbijin da radiyo na ‘ Human Right’ wato kare yancin dan Adam, Ahmed Isah ya ke yi a kasar nan.

Ahmed Isah yana daga cikin fitattu kuma shahararrun yan Najeriya da mutane musamman talakawa suke dogaro da wajen kwato musu hakki.

Idan har Allah ya ba ka damar yin ido hudu da shi ka kai masa kukan abinda yake damun ka, na damuwa, tauye hakki, bita da kulli, fin karfi, zalunci, da duk wani abu na cin mutunci da aka yi maka don an fi karfin ka, Ahmed Isah zai warware maka wannan matsala da ikon Allah.

Ya kai ga a yanzu da ka taba shi, har gara ka taba wani dan siyasan da yai suna a Najeriya.

Sai dai kuma a wannan bidiyo da aka fitar kuma ya karade shafukan yanar gizo, an nuno Ahmed ya gaggaura wa wata mata mari a filin shirin da yake yi duk safe a Abuja.

Ahmed ya fusata ne bayan taki amsa masa wasu tambayoyi game da wani mummunar laifi da ta aikata kuma ta amsa laifinta nan take bayan yan sanda sun damko ta.

Wannan mari da Ahmed ya daddalla mata ma su zafin gaske ne, masu kallo sun ji badi, sai dai laifin da ta aikata har ya fusatar da Ahmed ya daddala mata marin laici ne mai bada tausayin gaske.

Wannan mata dai ta kama wata yarinya kara ma da bata wuce shekara 7 ba ta danne ta da karfin tsiya ta daure mata hannaye da kafa sannan ta duldula mata kalanzir akai ta cinna mata wuta.

Idan kaga yarinyar, gaba daya kanta ya kone gashi nan danye.

Ganin haka Ahmed ya yi komarin danne zuciyarsa amma abin ya gagara bayan wanda ta aikata abin ta na ta cewa ita ma bata san me ya kai ta ga aikata hakan ba.

Duk da cewa wasu sun nuna marin matan da yayi a bainar talbijin bai dace ba, wasu na ganin da ma yayi mata abin da yafi haka.

” Duk wanda ya ga wannan yar yarinya sai ya tausaya mata.

” Ahmed daga aljihun sa kamar yadda ya saba ya cire kudi ya sa aka kaita asibiti kuma ya biya kudin aikin kan yarinyar. Wanda tana asibiti ana duba ta haryanzu, amma kuma lafiya ta samu.

Dayawa daga cikin wadanda suka kalli wannan bidiyo sun ce ba su abin bacin ko tashin hankali akai ba. Abin da Ahmed yayi ya yi daidai a wannan lokaci.

” Mata ce ta dildila wa yar karamar yarinya kalanzir aka ta cinna mata wuta akai, sannan don ya gaggaura mata mari sai a kawo wani wai ya ci mutuncin ta. Hakan da ya yi ma duk cikin kwato hakki ne. Sannan shine ya lale kudin sa ya kaita asabiti ga shi nan har ta fara wasan ta sosai. Ina gwamnatin suke, ina yan siyasa da masu kudin kasan? Talaka dai tsakanin sa da Ahmed Isah sai Allah ya saka da Alkhair. ”

Irin kyawawan ayyukan da yake yi wa talakawa marasa karfi a kasar nan ba su misaltuwa. Sai kwarara masa addu’o’i kawai masu karatu su ke yi bayan ganin abinda yayi da yi masa fatan Alkhairi.

Share.

game da Author