A karfafa wayar da kan matasa sanin illolin ta’ammali da muggan kwayoyi – Kungiyar Dalibai

0

Kungiyar dalibai na ‘Pan-African Student Union Parliament (ASUP)’ ta yi kira da a kara zage damtse wajen wayar da kan mutane musamman matasa sanin illolin dake tattare da shan muggan kwayoyi a kasar nan.

Kungiyar ta ce yin haka zai taimaka wajen inganta rayuwar mutane da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Kodinatan kungiyar Henry Nwankwo ne ya yi wannan kira da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Juma’a a garin Legas.

Nwankwo ya ce ta’ammali da muggan kwayoyi annoba ce dake addabar mu lalata rayuwar matasa a kasar nan.

Ya kara da cewa hakan na saka mutum cikin kuncin rayuwa, haukatar da mutum har yakan sa mutum ya kashe kansa.

Ya ce lalle ya kamata gwamnati ta gane cewa hukunta masu ta’ammali da miyagun kwayoyi ba shine maganin matsalar ba a kasar nan.

Wayar da kan mutane kan illolinndake tattare da ta’ammali da miyagun kwayoyi, shine mafita.

Nwankwo ya yi kira ga iyaye, masu ruwa da tsaki da gwamnati da a hada hannu domin ganin an kawar da wannan matsala daga kasar nan.

Kungiyar Pan-African Student Union Parliament (ASUP) kungiya ce dake shiga jami’o’i, makarantun koyar da aikin malunta da kwalejojin kimiya da fasaha domin wayar da kan dalibai da matasa sanin lillolin dake tattare da ta’ammali da muggan kwayoyi musamman ga lafiyar su.

Share.

game da Author