Ƴan bindiga sun sace ƴan makarantar Islamiya a Tegina, Jihar Neja

0

Ƴan bindiga sun sace yaran makarantar Islamiya da ba a san yawan su ba, ranar Lahadi a garin Tegina, Karamar Hukumar Kagara, Jihar Neja.

An ruwaito cewa ƴan bindigan sun kwace ofishin ƴan sandan garin sannan suka yi harbi sama kafin suka afka makarantar suka sace yaran dake karatun Islamiya.

Shugaban makarantar, Yakubu Idris ya bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES cewa ba zai iya fadin adadin yawan yaran s
da aka kwashe ba, amma har da kanwarsa aka ta tafi da.

Har yanzu rundunar ƴan sandan jihar ba su ce komai ba akai amma idan ba a manta ba karamar hukumar Kagara nan ne aka sace daliban makaranta wanda sai da aka yi ta kai ruwa rana da ƴan bindiga kafin suka sako su.

Share.

game da Author