Ƴan Jam’iyyar APC a Jigawa sun yi zanga zangar ƙin amince da ɗauki-ɗoran ƴan takara da uwar jam’iyyar APCn tayi a shirin zaɓen ƙananan hukumin da ake shirin yi a ranar 24 June.
An yi zanga-zangar ne a garin Kazaure inda dubban magoya bayan jam’iyyar suka yi Allah wadai da dakatar da Ɗan Majalisa, Muhammad Gudaji, wanda shima yayi kira ga shugaba Muhammadu Buhari yasa baki a daina kama karya a Jigawa.
Masu zanga-zangar ɗauke da kwalaya suna zargi gwamna Muhammad Badaru kakaba wa al’umma ƴan takara marasa farin jini harma da waɗanda suke zargin suna amsa tambaya a hukumar EFCC mai yaki da almundahana.
Masu zanga-zangar sun nuna goyon bayansu ga ɗan Majalisa, Muhammad Gudaji, wanda suka ce shi ne jagoran APC a masarautar Kazaure saboda ƙarbuwar sa ga jama’a.
Masu zanga-zangar sun yi jerin gwano ne saga unguwar kanti zuwa fadar Sarkin Kazaure amma daga bisani ƴan sanda sun hanasu ƙarisawa fadar sarkin.
Shugaban matasa na Jam’iyyar APC a ƙaramar ta Kazaure, Bilyaminu Lawan, yana daya daga cikin wadanda suka ƙarbi masu zanga-zangar, yace zasu kai dukkanin korafinsu ga uwar jam’iyya domin samun matsalaha.
A baya kafin zanga-zangar, Ɗan Majalissa Muhammad Gudaji, ya zargi gwamna Badaru da aikata ba daidai ba wajen fitar da ƴan takara da zasu fafata a zaɓen kananan hukumomi.
Gudaji Kazaure yace idan ba’a maida hankali ba za’a maimaita a Jigawa abinda kotu tayiwa APC a Jihar Zamfara ta kwace dukkanin kujeru ta baiwa jam’iyyar adawa saboda rashin yin zaɓen cikin gida.
Discussion about this post