ZAZZABIN CIZON SAURO: Yadda barayin gwamnati da kungiyoyi ke taya sauro kisan mutum 81,640 a Najeriya, duk shekara

0

Yayin da ake samu agajin kudi da kayan yaki da zazzabin cizon sauro daga Global Fund na makudan kudade, hakan bai hana sauro ci gaba da yi wa ‘yan Najeriya manya da kanana kisan kwaf-daya ba.

Dalili kuwa shi ne, wani kwakkwaran binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya tabbatar da yadda jami’an gwamnati da jami’an kungiyoyin harkar dakile zazzabin maleriya ke taya sauro kisan mutane, ta hanyar sace kayan da su ka kamata a raba wa talakawa kyauta, su na sayar wa ‘yan tireda.

Binciken PREMIUM TIMES ya gano yadda ake satar gidan sauro ana sayar wa ‘yan tireda da ‘yan kasuwar-tsaye, su na sayarwa, duk kuwa da cewa kyauta ake raba shi. Kuma an rubuta “KYAUTA, BA NA SAYARWA BA NE” a jikin kowane gidan sauron.

Kididdiga ta nuna cikin shekarun nan an samu koma-bayan shirin yaki da zazzabin cizon sauro a Najeriya, har ta kai a duk shekara akalla sauro na kashe mutum 81,640, wato kenan daga cikin mutum kimanin 400,000 da zazzabin cizon sauro ke kashewa a duniya, to kashi 20% bisa 100% (81,640) duk ‘yan Najeriya ne.

Duk da cewa an samu allurar zazzabin cizon sauro, amma dai kakaf a kasashe masu tasowa an yi ittifakin cewa gidan sauro shi ne babban rigakafin cizon sauro, mai hana sauro cizon da zai haddasa wa wanda ya ciza zazzabi.

Tsawon shekaru dai ana raba gidan sauro ne a karkashin NMEP, wato Shirin Kawar Da Maleriya Na Kasa.

Kungiyar Agaji da Jinkai ta Global Fund ke samar da kudade da gidajen sauron da ake rabawa.

Duk da a jikin kowane gidan sauro akwai rubutu gwara-gwara cewa: “BA NA SAYARWA BA NE”, wannan bai hana a rika sayar da gidan sauron a sassa daban-daban na kasar nan ba.

Binciken PREMIUM TIMES ya tabbatar da cewa jami’an aikin rabon maganin sauro da sauran kungiyoyi na da hannu wajen sayar da gidajen sauron da ya kamata a rika rabawa jama’a kyauta.

Wani mai sayar da gidan sauron mai dauke da sunan NMEP, a garin Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi, mai suna Mohammed Isa, ya sayar wa wakilin mu gidan sauro daya kan kudi naira 2,500.

Gidan sauron wanda wakilin mu ya saya a hannun sa, ya na da lamba:4956230886, kuma an rubuta “Ba Na Sayarwa Ba Ne” a jikin sa. Sannan kuma akwai tambarin Najeriya a jiki.

Isa ya ce daga Kaduna ake turo masa da lodin gidan sauron, ya na sayarwa a Ebonyi.

Isa dai ya fi tsayawa tallar gidan sauro a randabawul din Udensi, gaban tsohon gidan gwamnati.

Yayin da wakilin mu ya nemi ragi, sai Isa ya shaida masa cewa idan zai sayi da yawa, to zai iya sayar masa duk daya a kan naira 2,000.

Jami’in NMEP mai suna Emmanuel Shekarau, ya shaida wa wakilin mu cewa ba da sanin su wasu marasa kishi ke sayar da gidan sauron ba.

“Ko ma su wane ke kwasa su na sayarwa, a gaskiya ba su kyauta mana ba. Domin su na maida shirin yaki da zazzabin maleriyar cizon sauro baya matuka.” Inji Shekarau.

PREMIUM TIMES ta gano cewa a baya Global Fund ta taba zargin kungiyar SFH da harkalla.

Akalla cikin shekaru 10 an raba gidan sauro zai mai miliyan 500 a kasashen Saharar Afrika.

Daga 2000 zuwa 2012 an samu raguwar mace-mace sanadiyyar cizon sauro da kashi 42% bisa 100%.

Sai dai kuma yanzu daga shekarun baya-bayan nan lamarin ya lalace, har ana samun mutum miliyan 53 na kamuwa da zazzabin cizon sauro, inda a kowace sa’a daya tak zazzabin na kashe mutum 9.

Share.

game da Author