Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko reshen jihar Abia ASPHDA Chinagozi Adindu ya bayyana cewa zazzabin cizon sauro na haukatar da mutum idan mutum ya kamu da kuma ba a nemi magani da wuri ba.
Adindu ya fadi haka ne ranar Talata a hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a garin Umuahia.
Ya ce zazzabin cizon sauro na illata kwakwalwar mutum ta hanyar kumburar da magudanar jini a kwakwalwa.
Adindu ya yi kira ga mutane da su rika tsaftace muhallin su da rufe randunan da ake tara ruwa domin guje wa kamuwa da cutar.
Ya kuma ce hukumar su ta tsaro hanyoyin da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar a jihar.
Raba gidajen sauro, yi wa mutane gwajin cutar da bada maganin cutar, wayar da kan mutane game da illar cutar da hada hannu da ma’aikatar muhalli domin wayar da kan mutane mahimmancin tsaftace muhalli su na daga cikin matakan dakile yaduwar cutar da hukumar ta tsara kuma take yi.
Zazzabin cizon sauro cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cizon sauro
Alamun ta sun hada da zazzabi, ciwon Kai, rashin iya cin abinci, ciwon gabobin jiki da sauran su.
Cutar na iya yin ajalin mutum Idan ba a gaggauta neman maganin ba.
Bincike ya nuna cewa zazzabin cizon sauro na yin ajalin mutum 400,000 a Afrika duk shekara.
A Najeriya mutum miliyan 53 na kamuwa da cutar sannan cutar na yin ajalin mutum 81,640 a shekara.
Ranar 25 ga Afrilu rana ce da kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta kebe domin wayar da kan mutane game da cutar sannan da inganta hanyoyin dakile yaduwar cutar a duniya.
Discussion about this post