Kwamishinan lafiya na jihar Legas Akin Abayomi ya bayyana cewa duk shekara mutum 700,000 na kamuwa da zazzabin cizon sauro a jihar.
Abayoymi ya ce a jihar adadin yawan masu fama da cutar dake zuwa asibiti sun kai kashi 70%.
Ya ce a shekarar 2020 mutum 657,154 suka kamu da cutar a jihar.
Zazzabin cizon sauro cuta ce da ta fi yawan kama yara ‘yan ƙasa da shekara biyar da mata masu ciki.
Hakan na da nassaba ne da yawan cinkoson mutane, rashin tsaftace muhalli da sauran su da ake fama da su a jihar.
Abayoyi ya ce gwamnati za ta ci gaba da kokari wajen ganin ta zuba magunguna da ingantattun kayan gwajin cutar a asibitocin gwamnatin dake jihar.
Sai dai kuma duk da haka ya gargadi jami’an lafiya da su tabbata sun yi wa mutum gwajin cutar kafin a ba shi maganin zazzabin cizon sauro.
Bincike ya nuna cewa zazzabin cizon sauro na yin ajalin mutum 400,000 a Afrika duk shekara.
A Najeriya mutum miliyan 53 na kamuwa da cutar sannan cutar na yin ajalin mutum 81,640 a shekara.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa Najeriya za ta bukaci naira Tiriyan 1.89 domin dakile yaduwar cutar zazzabin cizon sauro a kasar nan.
Dakile yaduwar cutar ya hada da rage yaduwar cutar da kashi 10% da rage yawan mace-macen da ake samu a dalilin cutar zuwa kasa da kashi 50% daga cikin yara 1000 da ake haihuwa a kasar.
Ministan ya ce gwamnati ta tsaro wasu tsauraran matakan da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar a kasar nan.
Ya ce bisa ga lissafi zantar da wadannan matakai zai ci Naira tiriyan 1.89 sannan zantar da matakan a cikin wannan shekara zai ci Naira biliyan 352.
Ehanire ya ce kashi 63.1 na kudaden da gwamnati za ta bukata za a yi amfani da su wajen siyo magunguna, inganta aiyukkan jami’an lafiya domin samar wa mutane kiwon lafiya ta gari a farashi mai sauki.
Ya kuma ce za a yi amfani da kashi 35.9 wajen gudanar da bincike domin gano hanyoyin da suka fi dacewa wajen dakile yaduwar cutar.
Discussion about this post