Kwararrun jami’an lafiya sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ci gaba da wayar wa mutane kai wajen yin amfani da gidajen sauro da da maganin sauro cewa yin haka zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar.
Wadannan kwararrun sun yi wannan kira ne a wajen taron samar da hanyoyin dakile yaduwar cutar da aka yi a Abuja a makon da ya gabata.
Idan ba a manta ba a watan Disambar 2020 PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta gudanar ya nuna cewa an samu ragowan yaduwar zazzabin cizon sauro zuwa miliyan 9 a cikin shekaru 20 a kasashe 87 da suka fi fama da cutar.
Binciken ya kuma nuna cewa yaduwar cutar ya ragu daga miliyan 238 a shekarar 2000 zuwa miliyan 229 a duniya.
Zazzabin cizon sauro
Zazzabin cizon sauro cuta ce da ake kamuwa da ita a sanadiyyar cizon sauro wanda idan ba a gaggauta sama masa magani ba cutar ka iya yin ajalin mutum.
Cutar ta yi ajalin mutane da yawa a duniya duk da maganin warkar da cutar da ake da shi.
Zuwa yanzu nahiyar Afrika ce bangaren duniyan da wannan cutar ta yi wa katutu.
Sannan a kasashen Afrika Najeriya ce kasan da ta fi fama da cutar.
A shekaran 2019 WHO ta ce kimanin dala biliyan uku ne za a bukata wajen yaki da cutar amma kasashen da suka fi fama da cutar sun tara dala miliyan 900 kudin yaki da cutar.
Discussion about this post