ZARGIN RIDDA: Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a saki Mubarak Bala da aka tsare shekara daya saboda fita daga musulunci

0

Mashahuran masana ‘yanci da hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya (UN), su bakwai sun nemi a gaggauta sakin Mubarak Bala, mutumin Kano da ke tsare tsawon shekara daya a hannun ‘yan sanda bisa zargin fita daga musulunci.

Wannan kira wani karin matsin-lambar neman sakinsa ne, baya ga kiraye-kirayen da kungiyoyin rajin kare hakkain jama’a su ka rika yi, ciki kuma har da Amnesty International.

Mubarak, wanda ke tsare a Kano, zai iya fuskantar hukuncin kisa idan aka kama shi da laifi, bisa tsarin shari’ar musulunci, wadda wasu jihohin Arewacin kasar nan ke amfani da ita.

An kama Mubarak Bala a ranar 28 Ga Afrilu, 2020, a gidan sa da ke Kaduna, dangane da wani rubutu da ya watsa a shafin san a Facebook, wanda ake ganin batunci ne ga addinin musulunci.

An ce rubutun da Bala ya watsa ya haifar da bacin rai sosai a zukatan musulmin Arewacin kasar nan da dama.

Wani lauya ne mai suna S.S Umar ya shigar da korafi kan Mubarak Bala, tare da wasu malaman addini, har aka kama Bala a Kaduna, aka maida shi aka tsare a Kano.

Iyalan sa sun shafe watanni da dam aba su san inda ya ke tsare ba, sai daga bisani aka ba su damar rika ziyartar sa.

Ranar 20 Ga Disamba, 2020 Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, Iyang Ekwo ya bayyana cewa ana tsare da Bala bisa haramtacciyar hanya, don haka a gaggauta sakin sa.

Sannan kuma kotun ta nuna cewa hana Mubarak ya dauki lauyoyin da ya ke bukatar dauka, tauye masa ‘yanci ne da kuma hakki a matsayin sa na dan Najeriya, wanda ke a karkashin inuwar kwansitushin ta kasar nan.

Mai Shari’a Ekwo ya yanke hukuncin a bisa Bala diyyar naira 250,000 bisa tsare shi da aka yi.

Sai dai kuma hukumomin da abin ya shafa sun yi biris da wannan hukunci da Babbar Kotun Tarayya ta yanke cewa a saki Bala.

Wadannan masana na Majalisar Dinkin Duniya sun caccaki Najeriya dangane da danne hakkin dan Adam, da tauye masa damar yin abin da ya ga shi ke daidai a gare shi, kamar yadda dokar kasa ta bai wa kowa.

Wadanda su ka sa hannun neman a saki Bala, sun hada da Ahmed Shahedd, Mary Lawlor, Nils Melzer, Tlaleng Mofokeng, Morris Tidball-Binz da kuma Fernand de Varennes da kuma Diego Garcia-Sayan.

Share.

game da Author