Zaman dar-dar a kudancin Kaduna kan zargin mutuwar shugabannin Fulani uku da aka yi garkuwa da su

0

Idan ba a manta ba a cikin watan Maris ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka sace wasu shugabannin fulani uku a hanyarsu na dawowa daga taron sulhu da mazauna kauyukan karamar hukumar a fadar sarkin Zangon kataf.

Wadanda har yanzu ba a ji daga gare su ba kuma ake zaton sun rasu ne, sun hada da Pate Usman Kurmi, Wakilin Fulanin masarautar Atyap, Muhammadu Anchau, Ardo da aka gayyato daga jihar Bauchi, da Yakubu Muhammadu.

Mahara sun tare motar da wadannan mutane ke ciki bayan sun gama ganawa da wasu a masarautar Atyap. Daga baya an tsinci direban da wani mutum daya sai dai har yanzu ba a san ko sauran mutanen na raye ko mace ba.

‘Yan uwan su sun ce akwai yiwuwar duk an kashe su, tunda har yanzu ba a ji daga garesu ba.

” Mutane na ta yin tururuwa zuwa fadan basaraken Atyap din domin yi masa jajen shugabannin fulanin. Shima ya kai ziyara wajen iyalan Wakilin fulanin Atyap wanda daya ne daga cikin wadanda masu sarauta a masarautar sa.

Sai dai kuma kakakin ‘yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalinge, ya bayyana cewa ana kyautata zaton basu mutu ba domin har yanzu ‘yan sanda na neman su a cikin daji.

Share.

game da Author