Babban Daraktan Kungiyar Gwamnonin APC, masu kiran kan su ‘Progressive Governors’, Salihu Lukman, ya bayyana cewa APC za ta kasance ita ce jam’iyyar da za ta yi wa kan ta da kan ta adawar kayar da kan ta a zaben 2023 saboda dan karen rigingimu da sabanin da ke cikin shugabannin jam’iyyar.
Lukman ya yi wannan magana a ranar Litinin, a Abuja.
Lukman wanda aka sani da cewa ba ya saurara wa jam’iyyar su wajen yin furucin abin da ke zuciyar sa, ya bayyana cewa jikakka da tseren-tseren neman mukamai da ke cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC zai iya shafar nasarar jam’iyyar a babban zaben shugaba kasa da ke karatowa nan da shekaru biyu masu zuwa,
Ya ce ya hango jam’iyyar su ta APC za ta sha kaye a hannun PDP a zaben shugaban kasa na 2023.
“Duk manya da kananan ‘yan jam’iyyar APC masu kishi, kuma wadanda su ka zage damtse wajen rike amanar jam’iyya, tilas su nuna matukar damuwa ganin cewa sun kare martabar APC ta hanyar samar da bigire. To rashin wadannan a yanzu shi ne ainihin matsalar APC. Wannan jam’iyya dai matsalar ta na cikin ta baki daya.”
“Sauran jam’iyyu irin su PDP sun mutu, kwarangwal da rai ne kawai. Babban abin da su ke takama da shi domin su yi tasiri kawai shi ne yin amfani da rigimar da ke cikin APC, har su samu damar yin nasara a kan ta.” Inji Lukman.
Tun bayan da APC ta hau mulki dai cikin 2015 ta ke fama da rigingimu a tsakanin manyan ta da shugabannin jam’iyya, duk a wannan tsawon lokaci.
A zaben 2015, jam’iyyar ta samu nasara albarkacin soyayyar da talakawa ke yi wa Buhari.
Sai dai kuma yadda APC ta rasa gwamnonin jihohi da dama a zaben 2019, ya nuna cewa a zaben 2023, wanda za a tsaida takarar shugaban kasa ko gwamna, sai dai ya yi abin nan da Hausawa ke kira ‘iya ruwa fidda kai’, domin tasirin farin jinin Buhari ba zai yi wa dan takarar shgaban kasa ko gwamna da Sanata ko wani dan majalisar tarayya.
Wasu jihohin da APC ta rasa a zaben 2019 saboda matsalar rikicin cikin gida, sun hada da Zamfara, Bauchi, Adamawa da Oyo.
Lukman ya ce ya na tababa idan a yanu cikin APC akwai mai farin jini irin na Buhari, wanda zai iya tara mutane, magoya baya kuma masoya masu kaunar sa kamar irin yadda aka nuna wa Buhari a 20215 da 2019.