Za mu zaftare ma’aikatan gwamnatin Kaduna don samun kudin yi wa talakawa aiki – El-Rufai

0

Idan ba a manta ba Kananan hukumomin jihar Kaduna sun rage dubban ma’aikata a cikin makon jiya a jihar Kaduna.

Wannan rage ma’aikata da gwamnatin jibar tayi bai tsaya ga ma’aikatan kananan hukumomi ba domin a wata sanarwa da ta fito daga fadar gwamnatin jihar ranar Litini, wanda kakakin gwamnan Muyiwa Adekeye ya saka wa hannu, gwamna El-Rufai zai zaftare ma’aikatan gwamnatin jihar suma.

Baban dalilin da ya sa gwamna El-Rufai zai yi haka kuwa kamar yadda yake munshe a takardar, shine domin a samu kudaden da za a yi wa mutanen jihar aiki.

” Gaba daya kaf ma’aikatan jihar Kaduna ba su wuce mutum 100,000 ba, su kadai kawai suna cinye kashi 90 cikin 100 na na kudaden da jihar ke karba daga Abuja. Ba zai yiwu ace mutum 100,000 da iyalansu kadai su rika lakume kudin da ya kamata mutum miliyan 9 yan Kaduna su amfana da shi ba.

” A watan Maris din 2021 kawai cikin naira N4.819bn da jihar Kaduna ta karba daga Abuja, ta kashe naira biliyan N4.498 kawai wajen biyan ma’aikata ne. Ya saura naira miliyan 300 ne da ‘yan kai duk da haka ba a iya biyan sauran hakkokin aiki da kudaden harkokin yau da kullum.

” Ba an zabe mu bane kawai mu rika biyan albashi da kudin da za a rika samu. An zabe mu ne domin mu yi wa mitanen jihar Kaduna aiki, mu gina hanyoyi, mu inganta gari, mu gyara makarantu da asibitoci da samar da yanayi domin yan kasuwa su shigo jihar su saka jari. Wannan mutanen Kaduna sun shaidemu muna yi.

” Zaman Kulle da aka yi na Korona Bairos ya tona wa wasu asiri sannan ya nuna mana karara cewa bamu bukatar dandazon ma’aikatan dake cunkushe a ma’aikatun mu suna zaman kashe wando kawai da sunan wai suna aikin yi. Za mu zaftare irin wadannan ma’aikata harda wadanda gwamnati ta nada ‘Yan siyasa suma laujen mu bazi wuce su ba. Dama can basu komai sai su leko jefi-jefi wai suna aiki mu kuma muna narka musu kudi.

” Gwamnati ta sani cewa za a iya fadawa cikin matsaloli a lokacin da aka yi sallama irin haka. A jihar Kaduna zamu garzaya hukumomin tara kudaden Fansho da mutane ke ciki domin su gaggauta biyansu kudaden su, sannan kuma akwai dama da gwamnatin Kaduna ta bada na shiga tsarin shirn ayyukan gona da bada tallafi da take yi domin mutane su ci ribar abin kuma su amfana dashi.

Share.

game da Author