‘Yan sanda sun kama mutum 4 da ake zargi da yin garkuwa da mutane a jihar Adamawa

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu mutane hudu da ake zargi da yin garkuwa da mutane a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Suleiman Nguroje ya sanar da haka da yake zantaws da manema labarai a garin Yola ranar Laraba.

Nguroje ya ce an kama wadannan mutane a kauyen Garwayel dake karamar hukumar Hong.

Ya ce a watan Maris wadannan mutane sun yi garkuwa da Alhaji Yahaya Buba, Alhaji Sure da Alhaji Muhammed Bello dukkan su a kauyen Konto a karamin hukumar Gombi.

Nguroje ya ce a ranar 9 da 11 ga Afrilu rundunar ta saurari karar da wani ya shigar cewa wasu mutane na yi masa barazanar garkuwa da shi.

Mutumin ya ce mutanen sun aiko masa da wasikar cewa ya biya naira miliyan daya akan mutanen da aka yi garkuwa da su ko su zo su yi garkuwa da shi.

Da rundunar ta gudanar da bincike sai ta gano wani Adoneja Dauda mai shekara 30 dake zama a kauyen Hubbare a karamar hukumar Maiha.

Binciken ya nuna cewa Dauda ya karbi Naira 150,000 daga hannun Alhaji Dauda Hassan dake zama a kauyen Barkaji a karamar hukumar Hong.

Nguroje ya ce an kama Dauda da tsabanr kudi naira 86,000, bindigogi uku, wayoyi da layin waya.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Aliyu Alhaji ya ce za a maka su a kotu da zarar an kammala bincike akai.

Share.

game da Author