Kwana daya bayan da wasu tsagerun ‘yan bindiga su ka dira gidan Gwamna Hope Uzodinma su ka bude wa gidan wuta a kauyen su, wasu ‘yan fashi sun tare titi a cikin unguwar Orji da ke Owerri, kuma su ka dauki tsawon lokaci su na karbar kudade a hannun masu motoci, direbobin motocin haya da fasinjoji.
Lamarin ya afku a unguwar da tantagaryar ‘yan iskan Owerri su ka fi cin karen su babu babbaka, wato Orji.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan fashin sun kwaci makudan kudade, kuma sun harbi mutum hudu.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Imo, Orlando Ikeokwu ya shaida wa manema labarai cewa wadanda aka ji wa raunin an garzaya da su Babban Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) na Owerri ana kula da su.
‘Yan fashin sun rika yin harbi sama inda mazauna yankin da masu sana’o’i kowa ya arce a guje.
Yayin da yankin na jihohin kabilar Igbo ke kara rincabewa, Premium Times Hausa ta bada labarin yadda aka rasa rayuka a farmakin da sojoji su ka kai hedikwatar ESN, tsagerun tsaron IPOB.
Wata rundunar hadin gwiwar sojoji, ‘yan sandan mobal da SSS sun kai gagarimin samamen ragargazar tsagerun jami’an ESN, da Kungiyar IPOB ta kafa.
Hukumar Sojojin Najeriya sun ce daga cikin wadanda aka kashe a farmakin, har da Mataimakin Kwamandan Tsagerun ESN.
Akalla an kashe rayuka 11, ciki har da na jami’an tsaro hudu. Mataimakin Kwamandan ESN na cikin wadanda aka kashe.
Mohammed Yerima wanda shi ne Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya, ya fitar da sanarwar cewa an kashe mataimakin kwamandan tsagerun ESN mai suna Ikonson Commander tare da wasu tsageru shida.
Sanarwar mahukuntan sojojin ta ce an kwato zabga-zabgan makamai da kuma motocin sintirin tsagerun ESN, reshen ‘yan bindigar IPOB.
Sanarwar ta ce an kashe soja daya da ‘yan sanda uku. Kuma an kama tsageru da dama.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yafda mahara su ka kai wa gidan Gwamna Uzodinma na Imo hari da rokoki.
Wasu mahara da ba a san ko su wane ba, sun kai hari da manyan bindigogi rokoki a kan gidan Gwamna Hope Uzodinma da ke kauyen su, can a Omuma Oru, a Jihar Imo.
Ba Gidan Gwamnatin Jihar Imo aka kai wa harin ba. An kai harin ne gidan da gwamnan ya mallaka da ya gina a garin su.
Maharan sun kai harin a ranar Asabar da safe, misalin karfe 9 na safiya.
Sai dai har yanzu ba a san adadin yawan wadanda aka kashe a harin da aka kai wa gidan ba.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Imo, Declan Emelumba ya tabbatar da an kai harin, amma ya ce jami’an tsaro sun kori maharan.
“Wasu mahara dauke da manyan bindigogi, a cikin jerin gwanon motoci 15, wajen karfe 9 na safiyar yau Asabar, sun kai hari a gidan Gwamna Uzodinma da ke garin da aka haife shi.
“Sun yi kokarin banka wa gidan wuta, domin har da tsoffin tayoyi cike da mota kirar ‘tipper’ su ka je.
“Sun yi arangama fa jami’an bijilante da jami’an tsaron gidan. Amma an samu asarar rayukan wasu jami’an tsaro biyu. Daya Sajan na ‘Yan Sanda, daya kuma dan bijilante.”
Emelumba ya bayyana cewa sun hakkake wannan hari da aka kai ya na da nasaba da siyasa.
Jihar Imo kamar sauran jihohin Kudu maso Gabas, ta afka cikin rikicin fa ya kazanta sosai, tun bayan harin karya kofar gidan kurkukun Owerri da aka fitar da daurarru sama da 1,800.
An kuma kai wa ofisoshin ‘ysn sanda da dama hari a jihar.
Discussion about this post