Fitaccen Shehin malamin da ya yi suna wajen kokarin zama da ‘yan bindiga, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa dukkan rukunnan ‘yan bindigar da ya yi zaman sulhu da su, sun ajiye makaman su, kuma sun daina kai hare-hare da yin garkuwa da mutane.
“‘Yan iska da batagarin ‘yan bindigar da hukuma ta hana ni yin zama da su ne ke ci gaba da kai hare-hare da yin garkuwa da mutane.” Inji Gumi.
A cikin wata tattaunawa da Gidan Talbijin na Roots TV ya yi da Gumi, ya kara jaddada cewa shi bai ga sani aibi ba don ya ce a yi wa ‘yan bindiga afuwa, matukar yin hakan zai kawo karshen hare-hare, kashe-kashe da garkuwar da ake yi.
Ya ce ya hakkake dukkan maharan da ya zauna da su a dazukan da ya karade, sun ajiye makaman su. “Wadanda hukuma ta ki bari na zauna da su ne ke ci gaba da aika-aika, saboda gwamnati ba so ta ke na ci gaba da yin wannan sulhu ba.” Inji Gumi.
Yayin da wasu su ka rika jinjina wa Gumi dangane da yadda ya rika saida ran sa ya rika shiga dazukan Kaduna, Zamfara da Neja wajen kokarin zama da ‘yan bindiga, dimbin jama’a kuma sun rika zargin sa da alaka da su.
Idan ba a manta ba, Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya fito ya nuna rashin goyon bayan zaman da Gumi ke yi da ‘yan bindiga.
El-Rufai ya jaddada cewa tsakanin gwamnatin sa da ‘yan bindiga sai kisa kawai, babu batun sulhu ko biyan diyyar wadanda su ka yi garkuwa da su.
Gidan Talbijin na Roots TV ya tambayi Gumi makomar wadanda ‘yan bindiga su ka talauta, wadanda su ka kashe da sauran su, sai ya ce duk wannan ba zai hana a yi masu afuwa don a samu zaman lafiya ba.
“Ni kai na ‘yan bindiga sun zalunce ni. Sun kama dan uwa na, sai da mu ka biya miliyoyin kudi mu ka karbo shi. Sun kama dan direban da ya fi dadewa a duniya ya na tuka mahaifi na. Sun kama wasu kamar su takwas duk sun kashe su.
“Shin zan ce sai na rama ne a ci gaba da kashe sojoji, jami’an tsaro da sauran jama’a, ko a yafe, a sulhunta, a daina kashe-kashe? Wane ya fi alheri?”