‘Yan bindiga sun afka jami’ar Greenfield dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, suka sace dalibai dake makarantar.
Channels TV ta ruwaito cewa maharan sun arce da dalibai amma bata fadi yawan daliban ba.
Jaridar ta ce kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar mata da aukuwar wannan abin tashin hankali, amma bai fadi yawan daliban da aka sace ba.
Sanata Shehu Sani shuma ya yi tir da aukuwar wannan al’amari yana mai cewa ” Yanzu na karanta labarin wai an sace dalibai a jami’a mai zaman kanta dake Kaduna. Allah ya kyauta.
Wani ma’aikacin kamfanin Olam ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sun rika jin harbin bindiga cikin dare amma basu san me ke faruwa ba.
” Tsakani da Allah, ban ga dalilin da zai sa a halin da ake ciki wani ya bude makaranta a wannan wuri ba. Akwai hadarin gaske sannan kullum ka wuce za kaga motar yan sanda daya tilo a gaban makarantar.
PREMIUM TIMES ta nemi ji daga bakin kwamishina Aruwan da kakakin ‘Yan sandan Kaduna amma basu amsa waya ba.
Idan ba a manta ba a cikin watan Maris,’ Yan bindiga sun sace daliban makarantan Forestry,
Gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta biya ko sisi kudin fansar duk wanda aka sace a jihar.
” Ni fa koda da na ne aka sace, sai dai in yi masa addu’a Allah ya hada mu a Lahira, amma ba zan biya ko sisi ba.