A wata sanarwa da kwamishinan Tsaron Jihar Kaduna ya fitar ranar Juma’a maharan da suka sace daliban Jami’ar Greenland dake Kaduna sun kashe dalibai Uku.
Aruwan ya bayyana cewa yan bindigan sun jefar da gawarwakin daliban a wani kudiddifi a kauyen Kwanan Bature dake kusa da makarantar.
Gwamna El-Rufai ya yi tir da wannan kisa da aka yi wa daliban jami’ar. Kuma ya mika jajen sa ga iyayen wadannan dalibai.
‘Yan bindiga sun afka jami’ar Greenfield dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, suka sace dalibai dake makarantar.
Maharan sun arce da dalibai amma bata fadi yawan daliban ba.
Sanata Shehu Sani shima ya yi tir da aukuwar wannan al’amari yana mai cewa ” Yanzu na karanta labarin wai an sace dalibai a jami’a mai zaman kanta dake Kaduna. Allah ya kyauta.
Wani ma’aikacin kamfanin Olam ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sun rika jin harbin bindiga cikin dare amma basu san me ke faruwa ba.
” Tsakani da Allah, ban ga dalilin da zai sa a halin da ake ciki wani ya bude makaranta a wannan wuri ba. Akwai hadarin gaske sannan kullum ka wuce za kaga motar yan sanda daya tilo a gaban makarantar.
Idan ba a manta ba a cikin watan Maris,’ Yan bindiga sun sace daliban makarantar Forestry,
Gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta biya ko sisi kudin fansar duk wanda aka sace a jihar.
” Ni fa koda da na ne aka sace, sai dai in yi masa addu’a Allah ya hada mu a Lahira, amma ba zan biya ko sisi ba.
Discussion about this post