YAJIN AIKI: Ma’aikatan Shari’a sun garkame kofar shiga Kotun Koli a Abuja

0

Ma’aikatan Kotun Kolin Najeriya a Abuja sun hana gudanar da ayyuka da shari’u a kotun bayan da su ka garkame kofofin shiga kotun tun da sanyin safiyar Talata.

Sun fara wannan yajin aiki ne domin tirsasawa da matsa wa gwamnati lamba cewa a bar bangaren shari’a na kasar nan su rika cin gashin kan su, kamar yadda doka ta tanadar masu.

Ana sa ran wannan yajin aiki da dama su ka ayyana cewa za su fara a ranar Talata, zai shafi dukkan manya da kananan kotunan fadin jihohin kasar nan da Abuja da dukkan Ma’aikatar Harkokin Shari’a ta Tarayya da na jihohi.

Tafiya yajin aikin ya zo ne daidai lokacin da Kungiyar Lauyoyi ta Kasa ta roki ma;aikatan cewa kada su tafi yajin aikin, domin yin hakan zai kara gurgunta al’amurran kasar nan, ganinn cewa ba a gama murmurewa daga gaganiyar kokarin dakile cutar korona da illar da cutar ta haifar a kasar nan ba.

Wakilin PREMIUM TIMES ya isa bakin kofar shiga Harabar Kotun Koli a Abuja da karfe 7:10 daidai, amma ya samu kofar a garkame.

Ma’aikatan sun kulle kofar su ka bar ma’aikatan da su ka koma bakin aiki daga hutun bukukuwan Easter a tsaitsaye waje, babu damar shiga ciki.

An kulle kofar an kuma hana ma’aikatan NJC da FJSC shiga na su bangaren, wadanda ke cikin harabar gine-gine daya da bangaren Kotun Koli.

Cikin makon jiya ne PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Ma’aikatan Kotu da Ma’aikatun Shari’a na kasar nan sun kammala shirye-shiryen tafiya yajin aiki.

Labarin yanuna cewa dukkan ma’aikatan kotunan Najeriya da ma’aikatan da ke ma’aikatar shari’a dake karkashin Kungiyar Ma’aikatun Kotuna da Bangaren Shari’a, sun bada sanarwar shekawa yajin aikin da sai hali, domin su matsa lambar a bai wa bangaren shari’a cin gashin kai.

Ma’aikatan a karkashin Kungiyar JUSUN, wato Judicial Staff Union of Nigeria, sun fitar da wata sanarwa a ranar 1 Ga Afrilu cewa kada su sake su bari a bude kowace kotu a fadin kasar nan daga ranar Talata, 6 Ga Afrilu, 2021.

Sanarwar wadda kwafen takardar ya fado hannun PREMIUM TIMES, kuma Babban Sakataren JUSUN I.M Adetola ya sa wa hannu, ya umarci dukkan rassan kungiyar na kowace jiha da shiyya su tabbatar da sun bi wannan umarni.

JUSUN ta ce tun a ranar 13 Ga Maris, bayan sun tashi taro a Abuja, sun bada wa’adin kwanaki 21 ga gwamnati ta fara aiki da tarin cin gashin kan bangaren shari’a.

JUSUN ta yi kurari da barazana a lokacin cewa idan gwamnati ba ta fara aiki da tsarin ba bayan cikar wa’adin da ta bayar, to ma’aikatan kotuna a fadin kasar nan za su sake komawa yajin aikin da su ka dakatar, wanda idan su ka koMa yajin aikin a yanzu, ba a san ranar komawar su aiki ba.

‘Mu Fito Mu Kulle Dukkan Kotunan Najeriya Da Ma’aikatun Shari’a’:

“Ana umartar duk wani ma’aikatacin kotu da ma’aikatan ofisoshin shari’a su fito a ranar Talata mai zuwa, su kulle dukkan kotunan kasar nan a jihohin da su ke, har sai sun ji wani umarni daga Babbar Hedikwatar JUSUN daga Abuja, kafin su bude.”

Wannan yajin aiki ya kara wa ‘yan Najeriya shiga halin matsin da su ka shiga, tun bayan fara yajin aikin da kungiyar likitoci ta NARD su ka fara, kwanaki biyu bayan tafiyar Shugaba Muhammadu Buhari zuwa Landan domin ya ga likitocin sa.

Share.

game da Author