YAJIN AIKI: Ma’aikatan Kotu su daina dukan Gwamnatin Tarayya a kan laifin da Gwamnatocin Jihohi ke yi – Rokon Majalisar Tarayya

0

Kwamitin Majalisar Tarayya Mai Lura da Harkokin Shari’ da Kotuna, ya roki Kungiyar Ma’aikatan Harkokin Shari’a da Kotuna (JUSUN) da ta dubi Allah ta daina tsula wa Gwamnatin Tarayya bulala saboda laifin da gwamnatocin jihohin kasar nan su ka tafaka na kin bai wa kotuna cin gashin kai.

Shugaban Kwamiti Honorabul Luke Onofiok, dan PDP daga Jihar Akwa Ibom ne ya yi wannan rokon a zaman ganawar da kwamitinya yi da wakilan JUSUN a Abuja.

Su dai Ma’aikatan Kotu da Ma’aikatun Shari’a na kasar nan sun sheka yajin aiki ne tun makon jiya, bayan sun sha bada wa’adin neman biya masu bukatar su kafin su yanke shawarar tafiya yajin aiki.

PREMIUM TIMES ta buga labarin shirye-shiryen tafiya yajin aikin tun kafin su tafi, kuma ta buga dalilan tafiyar su yajin aikin.

Shi dai wannan yajin aiki ya durkusar da shari’un da ake gudanarwa a tarayya, jihohi da kananan hukumomi.

Sannan kuma ya haifar da tsaikon bayar da beli ko cinkoso a gidajen kurkuku, tunda sai kotu ce ke bayar da belin wanda aka tsare a kurkuku.

Dukkan ma’aikatan kotunan Najeriya da ma’aikatan da ke ma’aikatar shari’a da ke karkashin Kungiyar Ma’aikatun Kotuna da Bangaren Shari’a, sun bada sanarwar shekawa yajin aikin da sai hali, domin su matsa lambar a bai wa bangaren shari’a cin gashin kai.

Ma’aikatan a karkashin Kungiyar JUSUN, wato ‘Judicial Staff Union of Nigeria’, sun fitar da wata sanarwa a ranar 1 Ga Afrilu cewa kada su sake su bari a bude kowace kotu a fadin kasar nan daga ranar Talata, 6 Ga Afrilu, 2021.

Sanarwar wadda kwafen takardar ya fado hannun PREMIUM TIMES, kuma Babban Sakataren JUSUN I.M Adetola ya sa wa hannu, ya umarci dukkan rassan kungiyar na kowace jiha da shiyya su tabbatar da sun bi wannan umarni.

JUSUN ta ce tun a ranar 13 Ga Maris, bayan sun tashi taro a Abuja, sun bada wa’adin kwanaki 21 ga gwamnati ta fara aiki da tarin cin gashin kan bangaren shari’a.

JUSUN ta yi kurari da barazana a lokacin cewa idan gwamnati ba ta fara aiki da tsarin ba bayan cikar wa’adin da ta bayar, to ma’aikatan kotuna a fadin kasar nan za su sake komawa yajin aikin da su ka dakatar, wanda idan su ka koma yajin aikin a yanzu, ba a san ranar komawar su aiki ba.

‘Mu Fito Mu Kulle Dukkan Kotunan Najeriya Da Ma’aikatun Shari’a’:

“Ana umartar duk wani ma’aikatacin kotu da ma’aikatan ofisoshin shari’a su fito a ranar Talata mai zuwa, su kulle dukkan kotunan kasar nan a jihohin da su ke, har sai sun ji wani umarni daga Babbar Hedikwatar JUSUN daga Abuja, kafin su bude.”

Wannan yajin aiki ya kara wa ‘yan Najeriya shiga halin matsin da su ka shiga, tun bayan fara yajin aikin da kungiyar likitoci ta NARD su ka fara, kwanaki biyu bayan tafiyar Shugaba Muhammadu Buhari zuwa Landan domin ya ga likitocin sa.

A bangaren Majalisar Tarayya kuwa, Shugaban Kwamiti Onofiok ya jaddada cewa Majalisar Tarayya na goyon bayan ma’aikatan, amma kuma su daina abin da ake kira ‘kumburi ga doki, sakiya ga jaki.’

“Mu na rokon ku daina zabga wa Gwamnatin Tarayya bulala a kan laifin da jihohi su ka yi.”

Ya nemi shugabannin kungiyar JUSUN na kasa su nemi shugabnnin JUSUN na jihohi domin su tunkari matsalar daga tushe, wato daga jihohin su.

Share.

game da Author