Daya daga cikin manyan manazartan Chatham House da ke Landan mai suna Mathew Page, ya bayyana cewa manyan barayin da ke satar kudin Najeriya suna karkatar da kudaden zuwa Landan da Dubai ne ta hanyar fakewa da biyan kudaden karatun ‘ya’yan su da kuma sayen kadarori a kasashen biyu.
Page ya shawarci masu bincike cewa su maida hankali wajen binciken bangaren hada-hadar kadarori da kuma harkokin ilmi, inda ya ce ta can ake fakewa ana karkatar da kudaden da ‘yan siyasa ke sata daga Najeriya zuwa Dubai da Landan.
Ya bayar da wannan shawara a cikin wata takarda da ya gabatar wadda ya yi magana kan yadda ake fakewa da biyan kudin makaranta ana karkatar da kudaden sata daga Najeriya, ana sayen kantama-kantaman gdaje da kudaden a Landan da Dubai.
Laccar wadda Mathew Page ya gabatar a ranar Talata, ya samu halartar masana fannonin shari’a da hukumomin dakile rashwara da cin hanci, irin su ICPC.
Page ya bayyana cewa duk wasu hanyoyin kimshe kudaden Najeriya a Landan da Dubai ‘mustahabbai’ ne, amma manyan ‘farillan’ su ne hanyar da ake fakewa da biyan karatu kasashen waje a rika tura kudade a can. Daga baya a rika kwasar kudaden a can ana sayen kantama-kantama gidaje da su a Dubai da Landan.
“Yawancin gidajen da ‘yan siyasar Najeriya su ka saya a Landan da Dubai, ba da sunayen su su ka sayi gidajen ko kadarorin ba. da sunayen wasu ejan ne ko dangin su ko kuma kamfanin Shell.
“Akwai kantama-kantaman gidajen da barayin gwamnatin Najeriya su ka saya a Landan da Dubai sama da gidaje 800 na adadin da ya kai dala miliyan 400 a wadannan manyan birane biyu mashahurai na duniya.” Inji Mathew Page.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta taba buga makamancin wannan rahoton a lokacin da American Carnegie Endowment for International Peace su ka fallasa hanyoyin da ‘yan siyasar Najeriya ke boye kudi a kasashen waje.
An fallasa cewa ‘yan siyasar na kwasar makudan kudade da nufn samar wa ‘ya’yan su makarantu masu tsada, amma sai a karkatar da kudaden ana sayen gidaje a Dubai da Landan.
A na sa bangaren, Shugaban ICPC Bolaji Owasanoye ya bayyana cewa hukumar sa za ta yi bakin kokarin gano yadda ake fita da wadannan makudan kudade har gwamnati ba ta samun kudin shiga. Kuma ya ce za a kwato kudaden.